Daga MUKHTAR A. HALLIRU TAMBUWAL a Sokoto
Wata ƙungiya mai taimakawa mabuƙata da ake kira da Concerned Citizens of Likes Minds (CCLM) a turance, ta ƙaddamar da rabon tallafin kayan abinci da kayan karatu ga marayu da ɗalibai, ‘yan gudun hijira da sauran mabuaata, a Jihar Sakkwato.
Ita dai CCLM ƙungiya ce mai rassan a dukkan faɗin Nijeriya har da Jihar Sakkwato, wacce jama’a da dama ke amfana da ita, sakamakon tallafin da take bayarwa. A cikin ayyukan jinƙai da ƙungiyar ta gudanar a Sakkwato har da rabon kayan abinci a gidan marayu da sansanin ‘yan gudun hijira, tare da ƙaddamar da littattafan karatu da rubutu a wasu makarantu na jihar.
Babban Hafsan Tsaron ƙasa, Manjo Janar Christopher Musa shi ne ya bayar da tallafin kuɗaɗen da aka sayi waɗannan kayayyaki ta ƙarƙashin wannan ƙungiya, domin sauƙaƙawa jama’a saboda tsananin ƙuncin rayuwa da rashin tsaro da ake fama da su.
Sakataren ƙungiyar na ƙasa, Kwamred Ibrahim Riskuwa ya yi kira ga waɗanda suka amfana da wannan tallafi, su yi amfani da abinda suka samu ta hanya mai kyau, tare da jan hankalin ɗalibai da su mayar da hankali ga karatu wurin zama jakadu nagari abin alfahari ga Sakkwato da Nijeriya baki ɗaya.
