Wani Likitan Fida da ya ƙware kan dashen fatar mutum a ƙasar Indiya mai suna Dakta Subodh Kumar Singh da ake yi wa laƙabi da ‘Jarumin Likita’, yana samun yabo bayan ya yi tiyata ga sama da mutum dubu 37 kyauta don gyara tsagewar furucin yara da tsagewar leɓensu ko mokaɗewar leɓɓa.
A cewar Cibiyar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka (CDC), tsagewar leɓe da mokaɗewar ɓangarorin fatar baki, suna yin faruwa ne tun a lokacin haihuwa lokacin da leɓe ko bakin jariri ba su yi daidai ba yayin ɗaukar juna biyu.
Wannan na haifar da matsaloli iri-iri da suka haɗa da rashin samun madara a matsayin jarirai, kuma hakan na haddasa wa masu larurar haɗuwa da cin zarafi da nuna musu wariya.
Ana iya gyara nakasar da bayan haihuwa ta yin tiyatar gyaran fata (plastic surgery), amma hakan, ba su samuwa ga iyalai matalauta da suka fi buƙatarsu.
A Indiya dai an samu wannan likita a matsayin mai tallafa wa dubbban jarirai da yara, yana gyara tsagewar leɓɓansu ko ɓangarorin fatar bakinsu a kyauta, don haka ya ba su dama don samun ingantacciyar rayuwa.
An haifi wannan jarumin likita ne a cikin iyali masu tawali’u a garin ɓaranasi a Jihar Uttar Pradesh ta Indiya, Dakta Singh ya samar wa kansa nasara a lokacin ƙuruciya, inda ya sadaukar da aikinsa don taimaka wa mabuƙata, maimakon neman kuɗi.
Bayanai sun ce, bayan likitan ya rasa mahaifinsa, wani ma’aikacin jirgin ƙasa, lokacin da yake ɗan shekara 13, Singh da ’yan uwansa uku sun yi ta neman abin da za su ciyar da iyalansu ta hanyar sayar da kyandir da aka yi a gida da sabulu da tabarau a kan tituna da cikin shagunan unguwanninsu.
’Yan uwan Dakta Subodh sun daina karatu don su tallafa wa iyalansu, amma sun tabbatar da cewa Subodh ya ci gaba da karatunsa kuma ya cika burinsa na zama likita.
Kuma duk da cewa, yana taimakon ’ya’yan ’yan uwansa gwargwadon iyawarsa, ya yi ayyuka da dama a lokacin da yake neman ilimin.
Subodh ya kammala karatunsa a Cibiyar Kimiyyar Kiwon Lafiyar Jama’a, a fannin aikin tiyata na gaba ɗaya, kuma ya ƙware a aikin tiyatar sauya fata.
“Wahalhalun da suke fuskanta sun sa na fahimci halin ƙuncin rayuwa da suke fuskanta kuma na danganta su da su. Zama likita ya sa ni cikin matsayi na taimaka wa mutane da yawa. Ina so in kyautata rayuwar marasa galihu,” inji shi.
Fahimtar cewa jarirai da yaran da aka haifa da tsagewar leɓe ko mokaɗewa suna buƙatar taimako, sai likitan ya fara shirya cibiyoyin jinya kyauta tare da taimakon masu fama da cutar gwargwadon iyawarsa.
Ba da daɗewa ba aka fahimci ƙoƙarinsa ta hanyar ƙungiyar Smile Train, wata ƙungiya ta duniya da ta mai da a hankali kan yi wa yara tiyatar leɓe ko tsagewar fatar baki.
Tare da goyon bayansu da na sauran ƙungiyoyi masu zaman kansu, Dakta Singh ya iya taimaka wa ɗimbin mutanen da ya yi wa tiyata kyauta.
“Waɗannan jariran ba za su iya samun madara kamar yadda suke buƙata ba. Mutane da yawa suna mutuwa saboda rashin abinci mai gina jiki kuma sau da yawa ci gabansu ya takure. Yaran da wuya su yi amfani da harcensu wajen yin magana, hakan na haifar da matsalar magana,” inji Dakta Subodh Kumar Singh.
Tun lokacin da ya fara aiki da ƙaramin albashi a shekarar 2004, Dakta Singh ya yi wa yara da manya sama da dubu 37, tiyata kyauta tare da taimakon ƙungiyar Smile Train, ya kuma samu damar horar da waɗansu likitoci da dama a faɗin Indiya don gyara masu fama da matsalolin da suka shafi haihuwa da fatar wata rana za su iya kafa wata cibiya ta ƙasa don gyara tsagewar leɓe ta hanyar tiyata.
