Ɗalibi ya ɗirka wa matar shugaban jami’a ciki

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani ɗalibi mai mataki karatu na ajin 300, wanda ke karatun shari’a a wata jami’a da ba a bayyana sunanta ba a jihar Kogi, ya ɗirka wa matar shugaban jami’ar ​​ciki.

A cewar labarin da aka yaɗa a Facebook da kuma shafin Tuwita, matar shugaban jami’at, wadda ta shafe shekaru 18 tana neman haihuwa, yanzu ta kusa haihuwar ɗanta na fari.

Sai dai labarin cewa ɗalibi ne da alhakin ɗirka wa matar ciki ba wai mijinta ba, ya jefa al’ummar jami’ar cikin ruɗani.

By ukarofi