
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa na Katsina ya nanata aniyarsa ta bai wa ƙananan hukumomin jihar damar cin gashin kansu.
Raɗda ya faɗi hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙoncin tawagar ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta (ALGON) ƙarƙashin shugabancin Injiniya Bello Lawal Ƴandaki, a gidan gwamnatin jihar.
Gwamnan ya nuna jin daɗinsa akan zaɓar ɗan jihar Katsina (Bello Yandaki) a matsayin shugaban ƙungiyar, wadda ya ce nasara ce ga al’ummar jihar Katsina, da ma Arewacin ƙasar baki ɗaya.
Ya bayyana cewa a shirye yake ya kawo gyara ga dukkan wani tsari da ya shafi ƙananan hukumomi, don bas u damar tsayuwa da ƙafafunsu.
Raɗɗa ya kuma ce a shirye ya ke ya bai wa ALGON goyon baya wajen tafiyar da al’amurransu kuma ƙofarsa a buɗe take a duk lokacin da suke buƙatar gudummuwa ko shawararsa.
A jawabinsa, Shugaban ALGON kuma shugaban ƙaramar Kaita, Bello Lawal Ƴandaki, ya bayyana ziyarar a matsayin wata nasara da suka samu ya kuma ce gwamna Raɗɗa shi ma ya taɓa zama ɗaya daga cikin ƴaƴan ƙungiyar a lokacin da ya ke shugaban ƙaramar hukumar Charanchi.
Ya kuma yi godiya ga gwamnan bisa gudummuwa da goyon bayan da ya ba shi a lokacin da ya ke neman shugabancin ƙungiyar.
Ziyarar ta samu halartar sabon shugaban hukumar NEPAD, Hon. Jabiru Abdullahi Tsauri, ƴan majalisar zartarwa na jihar da tsohon shugaban ALGON wanda ya sauka Hon. Aminu Mu’azu Maifata, Ibrahim Dasuƙi Jalo da sauran jagororin ƙungiyar.
