An rantsar da Hon Abdulkadir Mamman Nasir a matsayin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya rantsar da Hon Abdulkadir Mamman Nasir a matsayin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar da masu ba gwamnan shawara guda uku .

Hon Abdulkadir Nasir tsohon ɗan majalisar wakilai a tsakanin 2007 zuwa 2011 kuma ya riƙe shugabancin jam’iyyar APC na jihar Katsina.

Kafin wannan muƙami shine babban daraktan na hukumar kula da noman rani a jihar,haka kuma ya riƙe muƙamin shugaban ƙaramar hukumar Malumfashi.

Hon Nasir da aka fi sani da suna (Andaje) ya taɓa rike muƙamin mai ba gwamna shawara kan tallafawa masu ƙanana da matsaikaitan sana’o’i.

Sauran waɗanda aka rantsar sun haɗa da Mustapha Bala Batsari a matsayin mai ba gwamna shawara kan cigaban kasuwanci da Hajiya Bilkisu Suleiman mai bada shawara kan harkokin Banki da kuma Ahmed Nasiru mai bada shawara kan raya karkara.

Da yake jawabin sa gwamna Raɗɗa ya buƙaci sabbin jami’an gwamnatin da su kwatanta gaskiya da adalci wajan sauke nauyin da Allah ɗora masu.

Da ya juya kan tsohon shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Jibir Ibrahim Tsauri kuwa gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana shi a matsayin haziƙi kuma babban abokin sa da yaji daɗin aiki da shi .

“Na tabbata Jabiru Ibrahim Tsauri zai taka rawar gani a sabon wajan aikin sa a matsayin sa na ƙwararre a aikin gwamnati”Raɗɗa yace

Da yake jawabin godiya Jabiru Ibrahim Tsauri wanda ya sami muƙamin shugaban hukumar cigaban Afrika (NEPAD)ya miƙa godiyar sa ga gwamna Dikko Raɗɗa da majalisar zartarwa ta jihar da damar da aka bashi a bautawa jihar.

Ya kuma ƙara godewa Dikko Raɗɗa bisa rawar da ya taka wajan sabon muƙamin NEPAD da ya samu.

By ukarofi