Hukumar NSCDC ta Zamfara ta kama wani ɗan Kano bisa laifin sata

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Rundunar ‘yan sandan farin kaya ta Nijeriya, sibil difens, reshen Jihar Zamfara, ta cafke wani mutum mai suna Muhammad Dauda Ismail daga ƙaramar hukumar Dala ta jihar Kano, da ake zargi da laifin sata da zamba cikin aminci.

Kwamandan rundunar a jihar, Muhammad Sani Mustapha ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai a Gusau yau Talata.

“ Alkasim Muhammad Kabir ɗan shekara 33 dan asalin Kano, wanda aka yi masa sata, a ranar Alhamis, 12 ga Disamba, 2024 ya kawo rahoton ɓacewar wata mota ƙirar Mercedes-Benz C300 mai lamba DAL68HK Kano da wayoyin shi guda biyu (Samsung Galaxy A55 5G & IPhone 12 “. Yace

A cewarsa, kafin a kama shi, an bin diddigin wasu guraren da mai laifin ya bi, musamman hanyar Dayi-Malumfashi- Futua ya nufi Jihar Zamfara daga Jihar Kano.

“A bisa wannan tallan da aka yi a kafafen sada zumunta rundunar ta gaggauta gano lamarin inda ta kama wanda ake zargin a Gusau ranar Lahadi 15 ga Disamba, 2024 da misalin ƙarfe 11 30 a wani gidan abinci da ke kusa da Masallacin Umar Bin. Khattab (Masallacin Kanoma).”

Ya kuma bayyana cewa wanda ake zargin Muhammad Dauda Ismail a hannun sa ne hukumar leƙen asiri da bincike ta gano motar da aka sace (Mercedes C300) da kuma waya (Samsung Galaxy A55 5G) da kuma kuɗi dala dubu bakwai (7000USD) na jabu.

A wata hira da manema labarai, Muhammad Dauda wanda ake zargin ya amsa cewa ya mallaki waɗannan kayayyaki ne ta hanyar yaudarar abokin nashi da cewar zaije ya cika gas (LNG) a wani kamfanin iskar gas a Kano amma ya arce.

Ya ce ya yi yunƙurin siyar da motar da wayoyin da ke hannun sa amma ya faskara saboda rashin gaskiya da kuma takardardun bayanan motar yayin da ya sayar da wayar IPhone 12 inda bi diddigi ya tabbatar da cewa, wayar a yanzu tana Lokoja ne a Jihar Kogi.

Kwamanda Sani Mustapha ya bayyana cewa, ana nan ana gudanar da tuntubar waɗanda suka sayi wayar domin karɓo ta saboda wanda ya saya ya amince ya mayar wa mai shi.

Ya bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike, wanda ake zargin za a gurfanar da shi a gaban kotu.

A halin da ake ciki, Shugaban NSCDC ya bayyana cewa, duba da bukukuwan Kirsimeti da ke gabatowa, rundunar ta tura jami’ai 550 domin wanzar da zaman lafiya a faɗin ƙananan hukumomi goma 14 na jihar da cibiyoyin ibada.

By ukarofi