Gwamnatinmu ta yi ƙoƙarin toshe hanyoyin zurarewar kuɗi a Kano – Gwamna Abba

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya ce gwamnatinsa ta yi ƙoƙari wajen ganin ta toshe hanyoyin zurarewar kuɗi mai yawa dan inganta hanyoyin kuɗin shiga a jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen taron tunawa da ranar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Duniya da Hukumar karɓar Ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da Cin hanci da Rashawa ta jihar ta shirya.

Gwamnan ya ce dole ne ya yi alfahari da hukumar ƙarƙashin jagorancin Barista Muhuyi Magaji Rimin-Gado bisa ƙoƙarinsa na aiki tuƙuru wajen aiki da masu cin hanci da rashawa a Kano.

”A yanzu duk wanda ya san jihar Kano, ya san bakin gwargwado mun yi ƙoƙari wajen yakar cin hanci da rashawa a wannan jiha mai Albarka.”

”Ya zuwa yanzu ma mun shirya sosai wajen ganin mun bai wa jami’an tsaro da Hukumar yaƙi da Cin hanci da Rashawa ta Jihar Kano dukkan goyon bayan da ya kamata wajen gudanar da aikinsu”, inji Abba.

Ya kuma buƙaci hukumomin dake yaƙi da cin hanci da rashawa a mataki na ƙasa da su shigo don haɗa hannu da gwamnatin jihar domin cigaba da yaƙar mugun ciwon dake damun al’umma.

A jawabinsa, Shugaban Hukumar yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta jihar Kano, Magaji Rimin Gado, ya bayyana irin nasarorin da hukumarsa take samu da irin goyon bayan da Gwamna Abba ya ke basu wajen gudanar da ayyukansu.

Kazalika, ya ce hukumarsu za ta cigaba da ƙoƙarin domin ganin an kawar da Rashawa baki daya a jihar.

By Babaji