Gwamnan Kaduna ya mayar wa iyalin Abacha filaye da gwamnati El-Rufai ta ƙwace

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya mayar da filaye guda biyu da ke cikin birnin Kaduna ga iyalin tsohon Shugaban ƙasa, Janar Sani Abacha, shekaru biyu bayan da tsohon gwamna Nasir El-Rufa’i ya ƙwace su.

Filayen da aka mayar sun haɗa da ɗaya da ke No. 9 Abakpa GRA, Kaduna, mai girman mita 2,284, wanda ke ɗauke da takardar mallakar gwamnatin Jihar Kaduna mai lamba 30575, da kuma wani filin da ke No. 1 Degel Road, Ungwan Rimi GRA, Kaduna, mai girman murabba’in mita 3,705, da ke ɗauke da takardar mallakar gwamnati mai lamba 11458.

Lauyan iyalin Abacha, Reuben Atabo (SAN), ya shaida wa manema labarai cewa an soke mallakar filayen ne a shekarar 2022 a lokacin mulkin tsohon Gwamna Nasir El-Rufa’i.

Gwamnatin Jihar ta wallafa sanarwa a jarida a ranar 28 ga Afrilu, 2022, tana mai cewa: “Ana sanar da jama’a cewa mai girma, gwamnan Jihar Kaduna, ya yi amfani da ikon da doka ta ba shi ƙarƙashin dokar Land Use Act ta 1978, ya soke mallakar filaye a cikin birnin Kaduna saboda wasu karya ka’idoji na amfani da filayen.”

A cewar Atabo (SAN), sunan Sani Abacha yana lamba ta 34 a jerin sunayen waɗanda aka soke musu filaye a sanarwar.

Don haka, Atabo ya garzaya Babbar kotun shari’a ta Jihar Kaduna da ƙarar KDH/KAD/465/2021 da KDH/KAD/509/2022 domin neman diyya saboda kunya ga sunan iyalin Abacha a cikin wallafar, da wasu ƙorafe-ƙorafe.

Sai dai, cikin hikima, gwamna Sani ya aika wasiƙu guda biyu a ranar 10 ga Disamba, 2024, ta hannun Mustapha Haruna, a madadin darakta janar na hukumar KADGIS, inda ya mayar da mallakar filayen tare da umartar masu mallakar su biya bashin kuɗaɗen da ake bin su.

By ukarofi