
Daga BELLO A. BABAJI
Shirin samar da abinci na duniya ƙarƙashin Majalissar Ɗinkin Duniya (MƊD) ya ƙaddamar da shirin bunƙasa damammaki ga sana’o’in nakasassu da bada kwangilolinta gare su.
Shugaban shirin, Daniel Kuhe ya sanar da hakan yayin wani taron gabatar da shirin wayar da kai ga tawagar masu buƙata ta musamman da aka yi a Abuja.
Kuhe ya bayyana buƙatar haɗin-gwiwa tsakanin hukumomin MƊD wajen samar da damammaki da daidaito acikin al’umma.
Ya ce yunƙurin zai taimaka wajen faɗaɗa hanyoyin damawa da ɓangarori daban-daban yayin ayyukan kwangilolin MƊD, ya na mai cewa nakasa ba hujja ba ce ta nuna wariya ga masu lalurar.
A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar ƙwararru kan harkar kwangiloli, Yusuf Iyodo ya bayyana yadda nakasassu ke fuskantar bambanci wajen gudanar da harkokin tattali a Nijeriya wanda hakan ya sa ba sa iya samun damar mallakar abubuwa masu daraja.
Ya ce akwai buƙatar a sanya su a sahun waɗanda za a bai wa damammakin samun kwangiloli a MƊD da kuma mataki na ƙasa musamman a kamfanonin da ke mallakin takwarorinsu ne.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta na cigaba da ƙoƙarin sauƙaƙe hanyoyin samun kwangila ga kowane ɓangare na al’umma domin inganta su.
