Tsaro, manyan ayyuka da Ilimi ke kan gaba a kasafin 2025 da Tinubu ya gabatar wa majalisa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Laraba ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 na Naira tiriliyan 47.9 ga ƴan majalisu a matakin tarayya.

Shugaba Tinubu ya lissafo ɓangarori daban-daban inda aka ware wa Tsaro tiriliyan N4.91, sai na Manyan ayyuka da ya samu N4.06tn, sannan ɓangaren Lafiya wanda ya samu N2.4tn, sai kuma N3.5tn ga Ilimi.

Ya ce batun abinci kuwa, ɓangare ne da bai buƙatar tattaunawa, ya na mai tabbatar da cewa gwamnatinsa ta na ɗaukar matakan da suka dace wajen ganin kowane ɗan Nijeriya bai kwana da yunwa.

Shugaban ƙasar ya ce 2025 ba lokacin bayani game da kuɗin shiga ko wanɗanda gwamnati ta kashe bane, lokaci ne na zartarwar.

Ya kuma ce harkar tattali abu ne mai muhimmanci ga ci-gaban ƙasa wanda a matakan da suke ɗauka akwai sauye-sauye na ci-gaba a ɓangaren.

Shugaba Tinubu yace kwanan nan ƴan Nijeriya za su fara girbar amfanin ci-gaba da aka samu a harkar tattali.

Haka kuma ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta cigaba da samarwa ɓangaren tsaro kayayyakin aiki na zamani da fasaha don ƙara wa jami’ansa ƙwarin-gwiwa da kuma inganta tsaro acikin ƙasa.

By Babaji