Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta ce ta tanadi isassun jami’an tsaro a faɗin ƙananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara, domin su tabbatar da gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin lumana a tsakanin mabiya addinin Kirista.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ASP Yazid Abubakar, ya bayyana haka a wata hira da ya yi da Blueprint ta wayar tarho a yau Laraba.
A cewar sa tuni rundunar ta kammala dukkan shirye-shirye na tabbatar da cewa dukkan majami’u sun samu cikakken tsaro don baiwa Kiristoci damar gudanar da bukukuwansu na Kirsimeti cikin lumana.
“Mun shirya tsaf domin tsara dukkan hanyoyin da za a tura isassun jami’an tsaro zuwa dukkan majami’u a kowane lungu da saƙo na jihar Zamfara, domin tabbatar da cewa Kiristoci zasu gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin tsari da lumana”. A cewar ASP Yazid
“Ina so in yi amfani da wannan kafar a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar Muhammad Dalijan, in yi kira ga mabiya addinin kirista da su kasance masu bin doka da oda tare da gargaɗin ‘yayan su da su guji aikata duk wani abin da zai iya haifar da tarzoma a lokacin bukukuwan Kirsimeti da kuma bayan bikin Kirsimeti a jihar. .” ASP Yazid yace
A cewar sa, rundunar ‘yan sandan za ta ci gaba da jajircewa wajen kare al’ummar jihar ba tare da la’akari da banbancin ƙabila, addini da yare ba, a lokacin bukukuwan Kirsimeti da kuma bayan bukukuwan Kirsimeti da ake gudanarwa a kowace ranar 25 ga watan Disamba.
“Za mu ci gaba da jajircewa wajen kiyayewa da kare rayuka, dukiyoyi da mutuncin ɗaukacin al’ummar Zamfara ba tare da la’akari da ƙabilarsu, addini da yarukan su ba ako yaushe musamman a lokacin Kirsimeti da kuma bayan bikin Kirsimeti da kuma bukukuwan sabuwar shekara”. Yace
