Daga AISHA ASAS
Abu Musa Al’ash’ari ya rawaito hadisi daga manzon rahman (S.A.W), cewa, Annabin Allah (SAW) ya ce, “Misalin aboki na gari da abokin banza, kamar misalin mai siyar da (ko daukar) turare ne, da mai hura zuga-zugi (kira), mai daukar turare ko dai ya shafa maka ko ka sayi turare a wurinsa ko kuma ka ji ƙamshi mai daɗi a wurinsa, mai hura zuga- zugi kuma ko ya ƙona maka kaya ko ka ji wari a wurinsa.” Wannan hadisi ne da Bukhari ya ruwaito.
Kamar yadda bahaushe ke cewa, zama da maɗaukin kanwa, shi ke kawo farin kai.
Bature na wata karin magana wai, ‘show me your friends, and I will tell you who you are ‘. Ma’ana, kalar abokanenka, kalarka. Idan kana so ka san waye mutum, to ka tambayi abokinsa, saboda kowanne aboki da abokinsa yake koyi.
Aboki na taka muhimmiyar rawa a rayuwar mutum, duk da cewa ba kasafai muka ɗauki hakan da muhimmanci ba.
Sau da yawa iyaye ke babban kuskure ta hanyar kawar da kai da irin yaran da ‘ya’yansu ke mu’amalanta, inda suke buga ƙirji cewa, sun ba wa ‘ya’yansu kyakkyawar tarbiyya da ba su da haufi kan duk irin abokan da za su yi ba za su wargaza ginin da suka yi. Dalilin kenan da ke sa su kawar da kai daga ‘ya’yan baƙotansu, a cewarsu, tunda na su sun gyaru, na kowa ma zai iya lalacewa.
Abu na farko da zan fara da shi shi ne, karin maganar Hausawa da ke cewa, ‘wake ɗaya ɓata gari yake’, wannan zai iya nuni da cewa, mummuna kan rinjaye kyakkyawa a saurin kwaikwayo.
Annabin rahma (SAW) ya ce, aljanna an kewaye ta da ababen ƙi, ita kuma wuta an kewayeta a ababen so. Ma’ana duk wani aikin da zai iya kusanta bawa da rahma yana da nauyi gare shi, kuma sai ya daure ne zai iya yin sa. Sannan a kullum yana yaƙar zugar shaiɗan kan rarashin da yake masa na barin wannan aikin da yake yi.
Wannan ne ya sa ko ɗanka na da kyawawan ɗabi’u, to yana da kyau ka dinga yi masa tuni lokaci zuwa lokaci, kasancewar yana tare da mai zuga shi kan ya bar alherin da yake aikatawa. Don haka da zaran zuciyar tasa ta ɗan raunana, sai ku zaburar da ita a matsayinku na iyaye ko malamai.
Kamar yadda aya a cikin littafi mai tsarki ta ce, “Ya ku waɗanda ku ka yi imani, ku yi imani.” Daga cikin darussan wannan ayar akwai tunatarwa, domin an kira waɗanda suka yi imani, sannan Allah Ya ce su yi imani.
Idan mun koma kan darasin namu, wannan bayanin zai ganar da mu cikin ‘yan watanni mugun aboki zai iya ɓata tarbiyyar da ku ka yi wa yaranku ta tsayin shekaru, domin yana da abokin aiki, wato shaiɗan, ga uwa uba zuciya na yin abun ne bisa tursasawa, don haka za ta bada tata gudunmawa idan ta samu wuri.
Dalilin kenan da ke sa idan yaro ko a makaranta ya mu’amalanci aboki mai himma ko son karatu, sai kaga ƙoƙarin sa ya ƙaru. Idan yana da son karatu ya shaƙu da aboki marar son karatu, to tabbas ƙoƙarin sa zai samu rauni ko yaya ne. Domin daƙiƙi na saurin tasiri akan mai ƙoƙari, kamar dai yadda idan ka sa garwashi a cikin toka sai shi ma ya zama tokar.
Da wannan nake kira ga iyaye kan ababe biyu. Na farko, ku kula da tarbiyyar ‘ya’yan makwotanku, domin kuwa idan sun gyaru, naka ma za su iya tsira da tarbiyyar da kuka ba su, idan kuwa sun lalace, da yiwar naka su bi hanyar da suka bi.
Don haka a lokacin da ka ga ɗan bakwocinka na aikata wani abu marar kyau, yi ƙoƙari iya yinka kaga an yi wa abin tubkar hanci, ko ba ka yi don Allah ba, ka yi don kuɓutar da ‘ya’yanka daga sharrin abinda zai iya zama a gaba idan babu kwaɓa.
Abu na biyu, ku bincike ko su wane ne abokan ‘ya’yanku, ma’ana duk wani sabon aboki da ku ka gani tare da yaranku, ku bincike ko daga ina suka fito, su waye iyayensu, da kuma halayyar su. Hakan zai ba ku damar sanin ko sun cancanci zama abokai ga ‘ya’yanku.
Sanin su waye abokan ‘ya’yanmu na daga cikin manyan taimakon da za mu iya yi masu don gyara duniyarsu da kuma lahira
