Babban labarin gabar ta tsakiya da ya karaɗe kafafen labaru shi ne kawar da gwamnatin Sham ta shugaba Bashar Al’Assad. Saurin mamaye yankuna har ta kai ga shiga babban birnin Sham, Damaskas ya ba da mamaki. Kama daga Hama, Aleppo, Homs, har mayakan su ka shiga Damaskas ba su samu wata turjiya ba daga sojojin gwamnati. Shin ina sojojin gwamnati su ka tafi ne ko me ya same su har a ka wuce ba su tare hanya ba abun dubawa ne. Wannan na nuna akwai alamu ƙarara na tun a baya Asad na samun taimakon ƙetare ne wajen kare gwamnatinsa. Bashar Al’Asad wanda ya kama madafun ikon Sham a shekara ta 2000 ya ma karɓi ragama ne bayan rasuwar mahaifin sa Hafeez Al’Assad. Wannan ya nuna gidan Assad ya yi mulkin Sham na tsawon shekaru 53. Wato Bashar ya yi mulki na tsawon shekaru 24 inda mahaifin sa Hafeez ya yi na shekaru 29. Mayaƙan Sham sun shafe shekaru da dama su na ƙoƙarin kawar da Bashar amma hakan ya gagara don yadda ya kan dau matakan murƙushe su.
Mayakan da su ka mutu a sanadiyyar wannan gwagwarmaya su na da daman gaske. Akwai hotunan da kan nuna sai an cika mota da gawawwaki a tafi da su don turbudewa. Gaskiya na yi mamaki da ya zama har yanzu da sauran mayakan da su ka iya sake taruwa har su ka kifar da gwamnatin Assad. Wani abun kula kuma shi ne yadda ƙasar Rasha ba ta kawo daukin da ta saba don kare Assad din ba. Ba lallai ya zama don ta maida hankali kan yaƙin Yukrain ba ne sai dai ta kan yiwu ta sauya matsaya kan Asad ɗin. Duk da haka yadda Bashar ɗin ya shiga Rasha don neman mafakar siyasa na nuna hulɗa ba ta kare ba tsakanin sa da shugaba ɓladimir Putin sai dai ba hulɗar ya cigaba da mulkin Sham ba.
In mun tuna a baya yayin da Rasha ke kai hare-hare da jiragen yaƙi kan mayaƙan don hana su ƙarfin da za su tunkari birnin Damaskas, ita kuma Amurka na ɗaukar matakan ƙarfafa mayakan ne. Abun da kai tsaye za a ce ya kawar da gwamnatin cikin sauri shi ne rashin samun tallafi daga ‘yan Hezbollah na Lebanon. Yaƙin da Hezbollah ta gwabza da Isra’ila kuma har yanzu bai dakata ba ya sa ba za ta ɗauki nauyin wani yakin ba. In mun tuna yaƙin ya yi sanadiyyar rasa ran shugaban Hezbollah din Hassan Nasrallah da sauran jagorori da ke fafatawa a ƙungiyar. A bangaren Iran kuma dama ta kan ƙarfafa wasu ƙungiyoyi ne don su kare muradun ta a yankin. Tun da Hezbollah na neman tallafin yaƙi da Isra’ila ne ba za ta iya tura dakaru zuwa Sham ba. Alaka da Lebanon ya sa wasu al’ummar Sham da wannan sabon yaƙin ya firgita sun fiuce inda su ka shiga Lebanon ɗin nan yayin da wasu kuma su ka yi ta gaggawar tara kayan abinci don kar a rufe kasuwa su rasa inda za su samu kayan masarufi.
Haƙiƙa yaƙin Isra’ila kan Gaza ya taimaka wajen karyewar gwamnatin Asad. Haka kurum fa Isra’ila kan iya tura jirage su yi ta ruwan wuta a cikin Sham harta kai ga wani lokaci ma ta kai wa wani ginin jakadancin Iran hari a Damaskas da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar wasu jami’an Iran ɗin. Za mu fahimci Isra’ila na yin abun da ta ga dama a yankin da sunan kare kan ta ko yakar abokan gaban ta. Bayan ma faɗuwar gwamnatin Asad, Isra’ila ta kai hare-hare cikin Sham ɗin da alamu ke nuna neman karya lagon duk wasu sauran muradun Iran ne a ƙasar.
Na ga wasu na rubutu da alaƙanta nasara ko akasin hakan ga bambancin aƙidar addinin Islama tsakanin ‘yan Sunnah da ‘yan Shi’a. Gaskiya ne Bashar na daga ‘yan Shi’a Alawiyya da ke nan Sham din inda mayaƙan kuwa ka iya alakan ta kan su da zama ‘yan Sunnah. Ko ma za a ce duk al’ummar Sham dai ka iya zama Larabawa kuma kasarsu ce ta gado da ya dace su dage wajen tsayawa da kafar su fiye da dogara ga wasu ƙasashe. Kazalika lallai-lallai ya dace Shamawa su dage kar su bari ƙasar su ta koma kamar Iraki bayan mulkin Saddam Hussein ko Libya bayan kisan gilla ga shugaba Moammar Ghaddafi. Ya zama mai muhimmaci su hada kai wajen dakatar da buɗe wuta. Har dai su ka raba kai to sa iya samun kan su a nadama. Ba abun da ya fi zama lafiya daɗi. Mayaƙan nan su yi adalci kar kuma wannan ya ce ya fi ƙarfin wannanko wancan ya balle ya yi can. Idan su ka yi aiki tare su ka kuma tare kutsen ƙetare ga sha’anin cikin gidan su waje da diflomasiyya to za su iya raya ƙasar su har tarihin ta na ilimi da arziki ya dawo.
Kasashen duniya na cigaba martani kan faɗuwar gwamnatin Assad:
Kasashen duniya na cigaba da martani kan faɗuwar gwamnatin Bashar Al’Asad na ƙasar Sham bayan hawa madafun iko tun shekara ta 2000.
Kalaman manyan shugabannin duniya na nuna yanayin yadda matsayar su ta ke kan faɗuwar gwamnatin da fitinar da ta aukawa gabar ta tsakiya ko kuwa kai tsaye yaƙin Gaza.
Yayin da wasu ƙasashen Larabawa ke bayyana nazartar lamuran da fatan samun maslaha a birnin Damaskas, ƙasashen yamma na bayanai da ke nuna Sham ta huta daga dogon mulkin kama karya na Assad.
Bashar Al’Assad dai ya yi farar dabarar ficewa daga ƙasar.kafin lamura su rincaɓe inda ya sauka a Rasha don samun mafaka mai inganci.
‘Yan ƙasar Sham za su so haɗa kai fiye da kowane lokaci a yanzu don samun sabuwar gwamnati da za ta kare muradun su.
A yayin da mayaƙa ke ƙoƙarin kafa gwamnatia sham, shi kuma firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce Isra’ila ba za ta dakatar da yaƙin Gaza ba a yanzu.
Netanyahu ya ce ya ɗauko burin gamawa da Hamas ne inda ya nuna fargabar dakatar da yaƙin zai sanya Hamas ta farfado ta kuma yaƙi Isra’ila.
Jagoran na ƙasar Yahudawa ya ce bas a son yanayin da Hamas za ta dawo da ƙarfin ta inda a ka shiga wata na 14 a na kai hare-hare a Gaza.
Sakataren wajen Amurka Anthony Blinken ya ce tun da Isra’ila ta karya lagon Hamas da ma kashe shugabannin mayaƙan, ya dace ta dawo da kamammun ta gida ta dakatar da yaƙin haka nan.
Duk da haka majiya kusa da Hamas na cewa Masar, Katar da Turkiyya na ɗaukar sabbin matakan tattaunawa don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.
ƙatar ta nuna kwarin gwiwa za a iya tsagaita wuta musamman don lashe zaben Amurka da Donald Trump ya yi.
Yaƙi kan Gaza ya yi sanadiyyar kashe fiye da Falasɗinawa 40,000 akasari mata da ƙananan yara.
Shugaban addinin ƙasar Iran Ayatollahi Khamenei ya zaiyana faɗuwar gwamnatin Bashar Al’Assad da shiri tsakanin Isra’ila da Amurka.
Khamenei ya ce a ɗakunan kulle-kulle ne ƙasashen biyu da kuma sa hannun wata makwabciyar Sham din wajen tallafawa mayaƙan har su ka kifar da gwamnatin Assad. A nan Khamenei bai ambaci sunan makwabciyar Sham ba amma an hakikance Turkiya ce. Shugaban addinin na Iran ya ce su na da shaidar kulle-kullen na shiyawa ƙasashen su ka yi wajen kawar da gwamnatin ta Damaskas. Turkiya da ke iko da wasu sassan arewacin Sham biyo bayan dogon lokaci na yaki da Kurdawan Sham YPG ta tamakawa mayakan wajen samun wannan nasarar. Duk da haka Iran ta buƙaci cigaba da hulɗa da sabuwar gwamnatin ta Sham bayan kawar da mulkin Assad da ta ke marawa baya. Iran ta bukaci sabuwar gwamnatin ta kunshi dukkan sassan ƙasar ta Sham. Khamenei ya bugi ƙirjin Iran ta na da ƙarfi kuma za ta cigaba da zama mai ƙarfi. Kazalika tasirin kawayen ta zai cigaba da bunƙasa don a cewar sa “duk lokacin da ka key akin gwagwarmayar sai ƙarfi za ƙara”
Yanzu dai Iran na da sauran mayaƙa da ke da tasiri a yankin wato ‘yan tawayen Houthi na Yaman. Sulhun da Iran ta yi da Saudiyya da kemarawa gwamnatin Yaman ta birnin Aden baya ya rage yawan hare-hare da labarun yaƙi na Houthi. An fi jin labarin houthi a hare-hare da ta kan kai kan muradun jiragen ruwa na dakon main a ƙasashen da ke marawa Isra’ila baya a yaƙin Gaza. Houthi kan cilla makamai kan jiragen ruwan Amurka da Burtaniya a nan Bahar Maliya. Manyan kasashen yamma kan yi ramuwa ta kai hari a sassan da houthi ke iko da su a Yaman ciki da babban birnin ƙasar San’a’a. Kuma a duk alamu na nuna tukun ƙasashen na yamma ba sa sha’awar gamawa da houthi don ba mamaki ta na taka rawar hana Saudiyya barci da ido biyu rufe da hakan zai sa Saudiyya ƙara ƙarfafa hulɗa da ƙasashen na yamma don kauda-bara.
Kammalawa;
Kwatar gwamnati ta hanyar gwagwarmaya na da amfani da akasin amfanin. Amfanin shi ne jagororin gwagwarmaya kan samu mara bayan jama’a don aiwatar da sauye-sauye kuma ba da wasu dokoki masu ƙarfi ba kamar yanda gwamnatin soja kan jingine tsarin mulki don ɗaukar wasu matakan ba sani ba sabo. Akasin amfani ya zama sun raba kai a samu zakuna biyu ko uku masu son madafun iko ko ra’ayin su ya zama shi ne kan gaba. Hakanan ta kan yiwu ƙasashen ketare da su ka tallafa su maida gwamnatin gwagwarmaya ta zama ‘yar amshin shatan su ko kare muradun su.
