Ɓarayi sun datse adireshin yanar gizo na Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa ta sanar da cewa ɓarayi a intanet sun datse adireshinta na yanar gizo.

A ranar Laraba ne hukumar ta wallafa hakan a shafinta na X.

Ta yi kira ga al’umma da ƙaurace wa duk wani bayani da za a yaɗa a ƙafar daga yanzu har zuwa lokacin da za a kammala aikin gyaran adireshin.

A halin yanzu jami’an gudanarwa suna ƙoƙari wajen ganin shafin ya koma aiki yadda aka saba kamar yadda suka tabbatar a sanarwar.

By Babaji