Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya sanya hannu a kasafin kuɗi na Naira biliyan 692.
Tun farko gwamnan ya miƙa wa Majalisar kasafin kuɗi na Naira biliyan 682 amma bayan da majalisar ta yi nazari da gyare-gyare ta ƙara Naira biliyan 10.
A bayanin sa gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa kashi 77% na kasafin kuɗin zai tafi ne wajan mayan ayyuka inda fanin ilimi yafi samun kaso mai tsoka.
Ya cigaba da cewa kasafin kudin mai suna “gina makomar alumma” zai maida hankali wajen harkar ilimi,noma da kiwon lafiya.
Malam Dikko Raɗɗa sai ya yabawa majalisar dokoki kan yadda tabi kasafin kuɗin sahu da ƙafa tare da gayyatar shugabanin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar domin kare kasafin kuɗin.
Haka kuma ya nuna jin daɗin sa yadda majalisar ta amince da kasafin kuɗin cikin lokaci da hakan ya nuna kyakkyawan dangantaka tsakanin majalisar dokoki da na zartarwa a jihar.
Gwamnan kuma ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na samar da abubuwan more rayuwa musamman a birane da karkara da kuma tabbatar da kowane ɓangare an dama dasu wajan tafiyar da harkokin gwamnati.
Kakakin majalisar dokoki Rt Hon Nasiru Yahaya a jawabin sa ya bayyana cewa majilisar ta bi duk dokoki da tsare tsare na majalisar kafin ta amince da kasafin kuɗin.
Ya ce kasafin kuɗin na 2025 alheri ne ga al’ummar jihar Katsina,sai yayi kira ga jama’ar jihar da su ba gwamnatin Dikko Raɗɗa goyon baya domin ta sami damar aiwatar da ayyukan raya ƙasa.
Kakakin majalisar ya jaddada goyon bayan ɗaukacin yan majisar da gwamnatin Dikko Raɗɗa wajan samar da shugabanci nagari.
