Har yanzu Lakurawa na cigaba da zama a Kebbi  

Spread the love

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi 

Tun lokacin da Lakurawa suka yi wa waɗansu mutane goma sha bakwai kisan gilla a garin Mera da ke ƙaramar Hukumar mulki ta Augie watanni biyu da suka wuce ne, al’ummar yankin suka sha alwashin bai wa garuruwansu tsaro ta hanyar amfani da ‘yan banga da mafarauta da sauran matasa masu jini a jika.

Ganin haka ne ya sa Lakurawan suka tattara nasu ya nasu suka bar sansanoni uku da suka kafa a ƙaramar hukumar mulki ta Augie da ke iyaka da jihar Sakkwato suka koma yankin Sakkwato, sai dai ba su bar kawo samame a yankin ƙaramar hukumar mulkin ta Augie suna tattara dabbobin mutane musamman shanu suna awon gaba da su ba.

Wata zantawa da wakilinmu ya yi da wani ɗan sakai daga yankin ya bayyana cewa gaskiya ne har zuwa yanzu Lakurawa ko kuma ɓarayin daji sun ɗauki sabon salon satar dabbobin mutane a wannan yankin musamman a garuruwan Tungar Tudu da kewaye da dai sauran ƙauyukan da ke kan iyakar jihohin Kebbi da Sakkwato ta ɓangaren ƙaramar hukumar mulki ta Augie saboda sau da yawa sukan bari sai hankalin mutane ya kwanta sai su laɓaɓo su kora shanu “wanda kafin a sanar da mu sun yi nisa saboda ba mu da babura sai mu kasa gane inda suke, amma dai muna sa ran akwai wani waje da idan sun kora dabbobin a kan zo da mota a kwashe su a wuce.”

Lakurawan ba su taɓa yin wani sansanin a wannan yankin na ƙaramar hukumar mulki ta Augie ba, sai dai suna shigowa ne daga jihar Sakkwato suna ta’adi sannan su gudu, duk da ya ke dai ba su da isashshen kayan aiki amma dai suna samun ƙwarin gwiwa daga shugaban ƙaramar hukumar mulki ta Augie Honarabul Yahaya Muhammed Augie a duk lokacin da suka nemi wani taimako wajen wannan aikin kai tsaye ya kan zo ko kuma ya turo wakilansa.

Ya bayyana cewa yanzu babban ƙalubale da ‘yan sakai ke fuskanta bai fi rashi ko kuma ƙarancin babura na shiga jeji ba saboda sojoji ba sa iya biyarsu su shiga jejin tare kuma motocin sojojin ba sa shiga jejin kwata-kwata, don haka su ke neman gwamnati musamman ta jihar Kebbi da ta taimaka musu da babura don kare al’ummar su da kansu ba sai sun jira an turo jami’an tsaro ba a duk lokacin da buƙatar shiga jejin ta taso.

Ya ƙara da cewa, “ba waɗansu sojoji da ke taɓuka wani abu saboda a kodayaushe suna nan bakin makarantar boko da ke bakin garin Mera amma dai maganar suna shiga jeji suna yaƙi da Lakurawan ba gaskiya ba ne, saboda a duk lokacin da muka shiga jeji tare da su sukan juyo su bar mu a can,” inji shi.

“Kuma wani abin ban haushi sai bayan ‘yan sakai sun samu wata nasara sai ka ji ana ta cewa wai sojoji alhali kuwa ba gaskiya ba ne.”

Bayanai daga ƙaramar hukumar mulki ta Arewa sun labartawa wakilinmu da cewa yanzu haka waɗannan Lakurawan suna nan suna harkokinsu a ƙaramar hukumar mulki ta Arewa musamman a yankunan da ke kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar da ke da manyan kasuwanni da suka haɗa da Gumki, Kangiwa Amagwaro zuwa Bachaka saboda a fili su ke shigowa cikin kasuwanni suna zagaye wani lokacin ma sukan yi sayayya.

Wani basarake daga ƙaramar hukumar mulki ta Arewa ya bayyana damuwarsa bisa ga irin cin zarafin da waɗannan mutanen ke yi saboda a cewarsa sukan shiga gida-gida suna kwance shanun mutane da ake kiwo da sauran kayan amfani suna tafiya da su. 

Sojojin da aka kawo domin kariyar mutuncinsu sun koma taron hanyoyi suna karɓar kuɗi hannun direbobi da masu Keke Napep da kuma babura maimakon su yi aikin da ya kawo su.

Kwanakin nan dai bayan samun waɗansu bayanai masu cin karo da juna kan maganar cewa Lakurawan sun karɓi ikon wani ƙauye da ke kusa da garin Kangiwa cibiyar ƙaramar hukumar mulki ta Arewa inda aka ce har sun naɗa Sarki an ga jirgin sojoji yana zagayen sararin samaniyar yankin.

By ukarofi