Ƙasashen da suka yi fice a fagen ƙwallon ƙafa a duniya

Spread the love

A jerin ƙasashen da suka yi fice a fagen wasan ƙwallon aafa, ƙasar Brazil ce a sahun gaba, Belgium ta biyu, Argentina ta uku, Faransa ta huɗu, Ingila ta biyar, Sifaniya ta shida, Italiya ta bakwai, Netherland ta takwas, Portugal ta tara, a yayin da ƙasar Denmark ta zo matsayi na goma, a cewar hukumar FIFA.

Hukumar ta kuma ce a ƙasashen Afrika, asar Senegal ita ce ta shatakwas a fagen tamaula a duniya, sai Morocco ta ashirin da biyu, Tunisia ta talatin, Nijeriya ta talatin da ɗaya, Kamaru ta talatin da takwas, Masar ta arba’in, sai kuma Algeria ta arba’in da ɗaya.

A wani labarin kuma, yayin da Amaju Pinnick ke shirin sauka daga muƙamin shugabancin Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya da ake kira NFF, bayan shekara 8, hukumar na ci gaba da shirye shiryen zaɓen wanda zai maye gurbinsa da za a yi ranar 30 ga watan Satumba.

Ahmed Sani Toro, tsohon babban sakataren hukumar ƙwallon ƙafa a Nijeriya, ya ce, kwamitin zaɓen da hukumar ta ƙafa ya fidda sunayen masu neman takarar kujerarsu ɗaya, ciki har da ’yan arewacin Nijeriya shida. Ya ƙara da cewa, ya zuwa yanzu zai yi wuya a yi hasashen wanda ake gani zai lashe zaɓen.

By ukarofi