Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban ƙungiyar Ma’aikatan ƙananan Hukumomi ta ƙasa, reshen jihar Katsina Alhaji Nasiru Wada ya taya tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari cika shekara 82 da haihuwa.
A wata hira da manema labarai a Katsina Alhaji Wada ya bayyana Buhari a matsayin shugaba na gari abin koyi da ba a taɓa samun shugaba mai gaskiya da rikon amana irin sa ba.
Shugaban NULGE a Katsina ya ƙara da cewa, Muhammadu Buhari tun yana riƙe da muƙamin ministan man fetur har ya riƙe muƙamin shugaban ƙasa har sau biyu ba a taɓa samun sa da rashin gaskiya ba.
“Shi yasa Buhari tunda ya gama mulkin sa ya dawo gida Daura yana zaune lafiya cikin kwanciyar hankali tare da iyalan sa’inji Wada.
Ya ƙara da cewa, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kawo gagarumin cigaba a kasa wanda wasunsu sai nan gaba ’yan Nijeriya za su gane.
Ya yi fatan Allah ƙara masa lafiya da nisan kwana.
