Shugaban ƙungiyar lauyoyin Kano ya yabawa ƙwazon babbar Alƙalin Alƙalan jihar

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD

An bayyana cewa zuwan Dije Aboki a matsayin  Babbar Alƙalin Alƙalan Jihar Kano, ɓangaren shari’a ya samu gagarumin ci gaba na mutumtaka.

Shugaban ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa reshen Ungogo a jihar Kano, Barista Ahmad Abubakar  Gwadabe ne ya bayyana hakan ga manema labarai a wani taro na ƙungiyar lauyoyi mata a Kano.

Ya yi nuni da cewa aikin tuƙuru da jajircewa akan gaskiya da kawo gyara a ɓangaren shari’a da babbar jojin take wala’alla shi ya sa sauran ƙungiyoyin Mata  musamman na lauyoyi suke duba suna koyi da ita. Domin shi ya gamsu mata za su iya yin abinda ya kamata a kowane fage  duba da irin matakai da babbar jojin jihar Kano take ɗauka na kawo gyara  a ɓangaren shari’a.

Batista Ahmad Abubakar Gwadabe ya ce a  shugabancin da yake na ƙungiyar lauyoyi na jihar Kano reshen Ungogo ya zo da wasu tsare-tsare  guda Bakwai da ya sa a gaba domin ya aiwatar dasu ɗaya bayan ɗaya wanda zai  zama kamar jagora gareshi domin duk lokacin da ake abu idan akwai manufa da  ake so a cimma, sai aga abubuwa sun zo cikin sauƙ,i wannan tasa suke ƙoƙarin tallafawa cigaban ƙungiyar.

Ya ce daga tsare tsare da suke son cimma sun haɗa da kare haƙƙin ɗan adam  da shine manufa gaba ɗaya na uwar ƙungiyar su, sannan  samun haɗaka da fahimta da ƙungiyoyi kamar irin su” FIDA” da hukumomin jami’an tsaro da kuma tarbiyantar da yan ƙungiyar kan wajen tsayawa da jajircewa akan gaskiya da bin doka.

Batista Ahmad Gwadabe ya ƙara da cewa kasancewar ƙungiyar tasu ta lauyoyi ta ƙasa reshen Ungogo basu da matsuguni na kansu  suna haya ne daga cikin abinda yasa a gaba akwai samar da matsuguni mallakar ƙungiyar  na dindindin da yardar Allah kafin wa’adin da aka zaɓe su na ya ƙare.

Ya bayyana cewa, reshe-reshe da ake dasu na ƙungiyar lauyoyi basu da bambanci yan’ uwan juna ne, duk suna tafiya a tsari na doka ne kowace jiha tana da dama tayi rassa sama da ɗaya kamar yanda a Legas suna da reshe sama da huɗu a babban birnin tarayya ma Abuja haka  a Kano suke  da reshe guda biyu na Kano da na Ungogo amma duka matsayin su ɗaya ƙarƙashin uwar ƙungiyar lauyoyin ta ƙasa.

Batista Ahmad Abubakar Gwadabe ya ce game da ƙorafi da ake yawan yi akan lauyoyi da alƙalai na gabatar da shari’a da ake samun suna karo da juna  suna yawan  kira ga lauyoyi da alƙalai a duk wata dama ta haɗuwa da suka samu akan  a daina irin wannan irin wannan karon a kotuna daban- daban da hakan ke haifar da matsaloli, musamman wajen bada umurni, wannan kotu ta yi na daban  wata ma ta yi na daban akan abu ɗaya.

Ya yi nuni da cewa akwai hukuma da take kula da Alkalai a matakin jiha da  ƙasa gaba ɗaya da ƙungiyar lauyoyyi ta ƙasa suna iya ƙoƙarin su wajen jan hankalin Alƙalai kuma idan aka samu da wani da  gangan wani alƙali ko lauya yana yin wani abu da ba daidai ba, suna ɗaukar mataki sosai akai kama daga  na jan kunne har ma  dakatarwa.

Da ya juya kan ƙaddamar da sabbin shugabannin  ƙungiyar mata lauyoyyi “FIDA” da mujallar su da   suka  wallafa karo na biyu da ya halarci taron  Shugaban ƙungiyar Lauyoyin reshen Ungogo  Batista Ahmad Abubakar  ya ce abu ne mai kyau  idan akayi la’akari da irin gudanarwa da suke bayarwa na tsayawa masu ƙaramin ƙarfi da ake cin zarafin su musamman mata da yara a gaban Shari’a don kwato haƙƙinsu.

Batista Ahmad Abubakar Gwadabe ya taya sabbin shugabannin ƙungiyar lauyoyi mata na jihar Kano da aka ƙaddamar ƙarƙashin jagorancin Batista Salma Danpappa murna da kuma jan hankalinsu su  ƙara kwazo da zage damtse akan irin ayyuka da suke musamman na tsayawa marasa ƙarfi kamar yadda shugabanni da suka gabata suke yi.

By ukarofi