An kammala babban taron masu aikin tattara Zakka da Waƙafi karo na huɗu a Jigawa

Spread the love

Daga MUKHTAR A. HALLIRU TAMBUWAL a Sakkwato

An gudanar da babban taron masu ruwa da tsaki na masu sha’anin karɓa da raba Zakka  karo na huɗu a garin Haɗejia da ke Jihar Jigawa. Taron wanda aka shirya da nufin haɗa kan ƙungiyoyi, hukumomi da kwamitocin zakka na jihohi, masarautu, da hukumomin gwamnatoci da masu zaman kansu, domin inganta yadda ake karɓa da raba Zakka ko Wakafi a Nijeriya.

Harwayau, taron ya samu halarta manyan mutane daga sassan ƙasar nan daban-daban, musammman masu hidimar Zakka da Waƙafi ko alaƙa da su, ciki har da tawagar  da suka samu zuwa daga Jamhuriyar Nijar.

Daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron akwai Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar, CFR, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Yayale Ahmad (Ajiyan Katagum) da Gwamnan Jihar Jigawa Umar A. Namadi, FCA, sai Mai Martaba Sarkin Haɗejia Dr. Adamu Abubakar, CON, tare da ɗaukacin sarakunan Jihar Jigawa.

Sannan kuma akwai wasu sarakunan da suka samu halartar taron daga maƙwaftan garuruwa irin su Sarkin Bade, Sarkin Lere, Sarkin Birnin Gwari, Sarkin Nguru, Tikau da sauran su. A lokacin taron masana sun gabatar da ƙasidu daban-daban, an kuma gabatar da rahotannin jihohi na yadda suke gabatar da ayyukansu da hanyoyin da suke bi, wajen tattara Zakka da raba ta.

An kuma karrama wasu hukumomi, kwamitocin Zakka har da masu zaman kansu da masarautun da suka yi zarra ga ayyukan Zakka.

Shugaban haɗakar kana Mataimakin Sakataren ƙungiyar Masu Aikin Tattara Zakka ta Duniya, Malam Muhammad Lawal Maidoki, Sadaukin Sakkwato, ya bayyana cewa wannan ƙungiyar ta cika shekara 10 kenan da kafuwa. An ga ɗimbin alfanun Zakkar da aka tara aka kuma raba ga mabuƙata a ɗaukacin sassan ƙasar nan ta biliyoyin naira.

Sannan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da ‘yan Majalisar ƙasa da na jihohi da su yarda su aiwatar da tsarin Zakka, domin fita daga ɗimbin matsalolin ƙasar nan.

A lokacin taron an samu damar ziyarar garin Guri, da Lafiya da ke Jihar Jigawa, inda aka fitar da Zakkar da wani Hakimi ya tara, ta sama da Naira miliyan 900, da ta shafi kayan abinci da dabbobi da kuɗaɗe. An kuma yi taron manena labarai a Kano, tare da halartar Sallar Jumma’a a Babban Masallacin Jumma’a na garin Haɗejia, wanda ya samu halartar Mai Martaba Sarkin Musulmi da Sarkin Haɗejia da ɗaukacin sarakunan Haɗejia.

Harwayau, Mai Martaba Sarkin Haɗejia ya shirya walimar cin abincin dare ga ɗaukacin mahalarta Taron, inda Sarkin na Hadeja ya karrama Mai Alfarma Sarkin Musulmi da ba shi wani takobi na musamman, domin bayyana jin daɗinsa da godiya da ziyarar Sarkin Musulmi.

Ya zuwa yanzu dai mun samu labarin dukkan maharta taron sun koma garuwaransu lafiya.

By ukarofi