Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) ya ce ya samu lamunin dala biliyan 1 da ɗanyen mai don tallafa wa aikin da aka sanya wa gaba na samar wa matatar Dangote gangar mai 650,000 a kowace rana.
Idan za a iya tunawa, Aliko Dangote, ya ce matatar man Dangote an gina ta ne ba tare da wani tallafi daga gwamnatin tarayya ba.
Dangote ya yi magana ne a taron 2024 na ƙungiyar Masu Mallakar ɗanyen Mai ta Nijeriya (CORAN), wanda aka gudanar a Legas a watan Oktoba.
“Mun gina matatar mai na Dangote ba tare da wani tallafi daga gwamnati ba,” inji shi.
“Don tabbatar da isassun kaya, za mu buƙaci dakatar da jinginar da mai. Abin takaici ne a yayin da ƙasashe irin su Norway ke sanya arzikin mai a kan gaba, a Afirka muna kashe kuɗaɗen da ake samu ta wasu hanyoyin,” inji Dangote.
Amma Babban Jami’in Sadarwa na Kamfanin NNPC, Olufemi Soneye, ya musanta ikirarin Dangote a taron masu ruwa da tsaki na harkar mai a Abuja ranar Litinin.
Da yake jawabi a yayin taron, Soneya ya ce, “Tsarin da aka yanke na samar da lamunin dala biliyan 1 da NNPC ke bayarwa, ya taimaka matuƙa wajen tallafa wa matatar man Dangote a lokacin da ake fama da matsalar ɗanyen mai, inda ta share fagen kafa matatar mai mai zaman kanta ta farko a Nijeriya.
“Wannan shiri ya nuna himma da kwazon kamfanin na NNPC wajen samar da hadin gwiwar jama’a da masu zaman kansu da ke kawo ci gaban kasa.”
Kakakin ya kuma ce kamfanin ya sauƙaƙe rancen dala biliyan 3 na Gazelle a matsayin wani muhimmin shiga tsakani don daidaita rikicin canjin waje na tarayyar.
Ya ce tare da shugabancin Mele Kyari, kamfanin NNPC ya samu nasarori masu yawa, inda ya sake fayyace yanayin harkar man fetur da iskar gas a Nijeriya.
“A ƙarƙashin jagorancin Mele Kyari mai hangen nesa, kamfanin NNPC ya samu nasarori masu inganci, inda ya sake fayyace yadda harkar man fetur da iskar gas ta Nijeriya ta kasance. Bugu da ƙari, Kyari ya ba da rancen dala biliyan 3 na Gazelle, wani muhimmin tsoma bakin da ya taimaka wajen tabbatar da zaman lafiyar tarayya a lokacin da ake fama da rikicin canjin kuɗaɗen waje,” inji Soneye.
