Rahoton IMF na 2024 ya cire Nijeriya daga ƙasashe 10 da suka fi tarin bashi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Sabon rahoton jami’an Hukumar Bayar Da Lamuni Ta Duniya (IMF) ya nuna ƙasashen Afrika da aka fi bi bashi a shekarar 2024 inda ya bayyana ƙasar Misira a matsayin wacce take da mafi girman kaso a Nahiyar da ya zarce Dala biliyan 9.

Rahoton ya nuna cewa a tsakanin watan Janairu zuwa Yuni na wannan shekarar, gwamnatin Nijeriya ta biya sama da Dala biliyan 2.24 na basussukan da ake bin ta wanda ya fitar da ita daga ƙasashen da bashi ya yi musu katutu.

Rahoton da kfishin kula da basussuka na Nijeriya ya fitar ya nuna cewa a watanni 3 na farkon 2024, gwamnatin Nijeriya ta biya Dala biliyan 1.12 na bashin da ake bin ta. A watanni 6 na shekarar ne kuma ta sake biyan Dala biliyan 1.12 ga ƙasashe da kuma hukumomin da ke bin ta bashi da suka haɗa da IMF da Babban Bankin Duniya.

Ci-gaban ya samu ne sakamakon matakin da gwamnatin Tinubu ta ɗauka na daina almubazzaranci da kuɗaɗen ƴan ƙasa musamman cire tallafin man fetur wanda ya taimaka wajen samun ƙarin kuɗaɗe ga jihohi da ma ƙasar baki ɗaya don ayyukan raya ƙasa da al’umma.

By Babaji