*Yadda Shugaba Tinubu ya yi wa ’yan Nijeriya dalla-dalla kan tsare-tsarensa
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A tattaunawar da Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi ta farko da manema labarai tun bayan ya ɗare kujerar shugabancin ƙasar a watan Mayun 2023, ya yi wa ’yan Nijeriya tulawar inda gwamnatinsa ta saka gaba, musamman a shekara mai kamawa ta 2025., inda ya ƙara jaddada aniyarsa ta cewa, babu gudu ba ja da baya kan manufofin nasa, lamarin da ya janyo cece-kuce a tsakanin al’umman ƙasar.
Yayin da wasu suka bayyana gamsuwa da yadda shugaban ya bayyana manufofinsa, wasu kuwa na ganin akwai buƙatar ganin ayyukan sun fara yin tasiri a zahiri kafin su yarda da alƙawuran da ya ɗauka.
A tattaunawar da ya yi da manema labaran a ranar Litinin, Shugaba Bola Tinubu ya ce ba ya nadamar cire tallafin man fetur da ya yi a farkon kama mulkinsa.
Shugaban na Nijeriya ya bayyana hakan ne a lokacin da aka yi masa tambaya kan ‘ko da ya fi kyau idan an jinkirta cire tallafin man fetur da kuma barin kasuwa ta tantance darajar naira’.
Tinubu ya ce “babu yadda za a yi na bari ana sayar da man fetur ta yadda ƙasashe maƙwafta za su riƙa samun garaɓasa. Ba na nadamar komai game da cire tallafin man fetur.
”Muna kashe abin da za mu amfana da shi a gaba ne, muna yaudarar kanmu ne kawai, wannan sauyi dole ne,” inji shi.
‘Ba na goyon bayan ƙayyade farashin kayayyaki’
Sannan ya ƙara da cewa shi ko alama bai yarda da tsarin ƙayyade farashi ba kuma ba zai yi hakan ba, illa dai za su yi aiki tuƙuru su tabbatar sun samar da man a kasuwa.
A ranar 29 ga watan Mayun 2023, lokacin jawabin karɓar mulki na Bola Tinubu ya bayyana cire tallafin man fetur.
Masana da dama na kallon cire tallafin man fetur da barin kasuwa ta tantance darajar naira a matsayin abubuwan da suka ta’azzara matsalar tattalin arziƙi da al’ummar ƙasar suka faɗa ciki.
Tun bayan cire tallafin farashin man daga kusan naira 200 a kan lita ɗaya zuwa sama da naira dubu ɗaya abubuwa suka ta’azzara ga ‘yan ƙasar kasancewar man ya damfara ga yawancin harkokin rayuwar al’ummar.
Nijeriya, ƙasar da ta fi yawan jama’a a Afirka shekara da shekara tana fama da matsalar mai, inda kusan dukkanin matatun man fetur ɗinta mallakar gwamnati kusan ba sa aiki.
Wannan ya sa ƙasar ta dogara kusan kacokan a kan man da ake tacewa a waje, inda kamfanin mai na ƙasar NNPCL, ke zaman babban mai sayo man daga waje, yayin da ita kuma take sayar da nata ɗanyen ga ƙasashen waje.
Haka kuma a dai wannan lokaci da gwamnatin ta cire tallafin ta kuma bar kuɗin ƙasar naira ta sama wa kanta daraja a kasuwar kuɗaɗen waje baya ga rage darajar kuɗin da gwamnati ta rinƙa yi.
Wannan ya sa darajar kuɗin ta yo ƙasa warwas daga matsayin dala ɗaya a kan naira 700 zuwa sama da dala ɗaya a kan naira 1600 a kasuwar bayan fage.
Wannan ma ya haifar da gagarumar hauhawar farashin kayayyaki da ‘yan ƙasar ba su taɓa gani ba.
‘Babu gudu babu ja da baya akan dokar haraji’
A yayin wannan tattaunawa ta musamman da manema labarai da shugaban na Nijeriya ya yi ya kuma jaddada matsayinsa a kan sauyin da ya sanya a gaba a kan haraji inda ya gabatar da ƙudurin doka ga majalisar dokokin ƙasar domin ta amince ya aiwatar, dokar da ta janyo taƙaddama a ƙasar musamman ƙin amincewa daga yankin arewaci lamarin da ya tilasta wa ‘yan majalisar tuntuɓa a kai.
Wannan matsin lamba da adawa da ƙudurin na Tinubu ta gamu da shi daga wasu gwamnoni da sanatoci, hatta ma daga cikin jam’iyyar APC ta shugaban ya sa ya ce a shirye yake da a tattauna a kan batun, ya kuma bayar da ƙofar yin hakan.
Ya ce amfanin ƙudurin dokar nesa ba kusa ba ya ɗara illolinsa, inda ya ƙara da cewa ƙuduri ne da zai amfani jama’a wanda zai kare masu rauni.
Tinubu ya ce babu maganar janye ƙudurin domin abu ne na kishin talaka kuma zai faɗaɗa yadda ake biyan haraji, ta yadda za a samu ƙarin jama’a da ke biya.
A dangane da wannan ma ya ce ba ta yadda zai ja da baya daga abin da yake da kyau da amfani ga jama’a.
Ya ce, ”alamar shugaba na gari ita ce iya jajircewa kan yin abin da ya wajaba ya yi a lokacin da ya wajaba a yi shi.
‘Nijeriya na kan turbar ci gaba’
Duk da irin katutun matsalolin da ‘yan ƙasar ke fama da su na tsadar rayuwa sakamakon sauye-sauyen da gwamnatin ke ɓullo da su, Shugaban na Nijeriya, ya bugi ƙirji da cewa ƙasar na kan turbar cigaba.
Tinubu ya ce tsawon wata uku a jere ya cimma buƙatun kuɗi na ƙasar ba tare da ya taɓa ko kwabo daga kuɗaɗen da kamfanin mai na ƙasar NNPCL ke samarwa ba, ko kuma karɓar kuɗi daga Babban Bankin ƙasar, CBN ba.
Hakazalika Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su yi wa shugabanninsu addu’a tare fatan samun ci gaba mai ɗorewa a ƙasar.
Wannan na cikin saƙon Kirsimeti da shugaban ya aike wa Kiristoci yayin da suke shirye-shiryen gudanar da bikin Kirsimeti na bana.
“Kirsimeti na tunatar da mu ƙaunar Ubangiji, zaman lafiya, da haɗin kai,” in ji Tinubu.
“Tana nuna mana cewa ci gaba zai iya bayyana duk da ƙalubalen da muke fuskanta.
“Yayin da muke bikin, mu tuna da waɗanda ke cikin wahala saboda munanan al’amura da suka faru kwanan nan kuma mu yi addu’a don samun lafiya da kwanciyar hankali.”
Ya nuna damuwarsa kan waɗanda suka rasa rayukansu a turmutsitsin da ya faru a Ibadan, Okija, da Abuja.
“Muna addu’a irin waɗannan munanan abubuwan ba za su sake faruwa ba,” in ji shi.
Shugaban ya kuma yi kira da a tausayawa waɗanda ke cikin ƙunci a wannan lokaci, tare da yaba wa sadaukarwar sojojin Najeriya.
“Sojojinmu da suke kare ƙasarmu sun cancanci goyon baya da addu’o’inmu,” in ji Tinubu.
“Tare, za mu iya sake gina Najeriya mai albarka.”
Tinubu ya yi wa matafiya fatan alheri, inda ya ce gwamnatinsa ta samar da jiragen ƙasa kyauta da rangwamen kuɗin sufuri a faɗin ƙasar domin sauƙaƙa tafiye-tafiye.
‘Ba zan rage yawan ministocina ba’
Shugaban na Nijeriya ya mayar da martani ga masu suka da ke cewa majalisar ministocinsa ta yi yawa, inda ya ce ba zai rage yawan ministocinsa daga 48 da suke a yanzu ba.
Tinubu ya kafa hujja da cewa ya zaɓi ministocinsa a bisa aiki tuƙuru saboda haka ba shi da niyyar rage su.
A watan Oktoba na wannan shekarar mai ƙarewa ne Shugaban ya sauya wa ministoci 10 wurare tare da naɗa wasu bakwai sababbi. Haka kuma ya sauke guda biyar, to amma duk da haka masu suka na cewa majalisar ministocin ta yi girma da yawa.
‘Yadda za ku rage yawan kashe kuɗin wutar lantarki’
Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya shawarci ‘yan Nijeriya kan yadda za su yi tsumi da dabara wajen rage yawan kashe kuɗin wutar lantarkin da suke sha.
Shugaban ƙasar ya shawarci ‘yan Nijeriya ne a yayin tattaunawa da manema labarai na fadar shugaban kasa na farko da NTA ta watsa a daren Litinin.
“Ba wani aibu ba ne koyon tattali. Ku koyi yadda ake tattalin yawan kashe kuɗin wutar lantarki, ku kashe ƙwayaye, mu koyi yadda ake sarrafa su,” inji Tinubu.
Bayan rantsar da shi a watan Mayun 2023, farashin makamashi ya yi tashin gwauron zabo, musamman wajen cire tallafin man fetur da ƙarin kuɗin wutar lantarki. Farashin man fetur ya ninka sau huɗu, inda ya tashi daga ƙasa da Naira 200 a kowace lita zuwa sama da Naira 1,100 a yawancin sassan ƙasar nan.
A ranar 3 ga Afrilu, 2024, hukumar kula da hasken wutar lantarki ta ƙara kuɗin wuta ga kwastomomin da aka ce suna ƙarƙashin tsarin Band A, inda yanzu kwastomomin ke biyan Naira 225 kilowatt a sa’a guda daga Naira 66, al’amarin da ‘yan Nijeriya da dama suka yi kakkausar suka, la’akari da yawan ƙarin kuɗin da kuma wahalhalun da ake ciki a ƙasar.
Tinubu ya kuma yi iƙirarin cewa rashin ɗa’a da rashin tsari ne suka haddasa tashe-tashen hankula a Oyo, Anambra da Abuja, inda mutane suka mutu yayin rabon kayan abinci.
“Abin takaici ne cewa mutane ba su da tsari sosai. Dole ne mu kasance masu ɗa’a a cikin al’ummarmu, mu jajenta wa waɗanda suka rasa ‘yan uwa,” inji Tinubu a lokacin da yake magana kan munanan al’amura da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
‘Ina da ƙwarin gwiwar magance matsalar tsaro’
Shugaba Bola Tinubu ya ce yana da ƙwarin guiwa akan mangance matsalar tsaron Nijeriya.
“Abin takaici ne matuƙa yadda aka yi wa jama’a kisan gilla a baya. Na tuna lokacin da na tsunduma yawon yaƙin neman zaɓe. Dole na dakatar da yaƙin neman zaɓen don ziyarar ta’aziyya a Katsina, Kaduna, da sauransu.
“Yau ga shi ana iya tafiya ta hanya. Kafin yanzu, ba zai yiwu ba.
“Ba za ka iya cewa sojoji ba su shirya ba a lokacin da aka kai wa bataliya ta brigade hari.
“Ba za ku iya yi wa ƙasarku dariya ba saboda haka; maƙiya ciki da waje suna kallon abin da kuke yi,” inji Tinubu.
