Me za mu tuna da 2024?

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

A kwana a ta tashi ba wuya da lafiya ko ma ba lafiya ga shi nan ita ma shekara ta 2024 ta na bankwana. Ai kamar jiya ne fa a ke batun zaɓen 2023 yau ga shi har an fara batun zaɓen 2027 in Allah ya kai mu. Shin mun ci riba ko ba mu ci ribar ba shekrarar dai ta kare. Ga dai dan Nijeriya na tabbata abu biyu za su fi zama kan gaba a shekarar wajen musamman masu sharhi wato tashin farashin kayan masarufi a babban sanadiyyar gauron zaɓin farashin man fetur sai kuma tattaunawa kan batun sabuwar dokar haraji da ke gaban majalisar dokoki da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura. Gaskiyar magana an yi hasashen farashin litar mai sai yah aura Naira 1000 kuma hakan ya tabbata.

Rayuwar kasuwanci ko tashin farashin kayan masarufi a Nijeriya na da alaka ta kusa da batun farashin man fetur. Hatta ma karin mafi ƙarancin albashi da a ka yi ya biyo bayan batun tsadar rayuwa saboda janye tallafin mai kuma gwamnati ya zama mai muhimmanci ta rarrashi ma’aikata da wannan karin. Ba a ma batun ko ƙungiyoyin kwadago za su kira yajin aiki ko kuwa a’a wannan ya shafi rayuwar miliyoyin mutane ne a birane da karkara. Idan ka ga wannan matsin bai shafi mutum ba to ka tabbatar rumbun sa dama a cike ya ke kuma zarar sa ba ta kare dami. Haƙiƙa masu matsaikacin samu ma na kuka ainun inda ’yan jari hujja su ka matse bakin aljihun su.

Da an ƙasa mutane kashi uku tsakanin masu hannu da shuni, matsakaitan masu samun kuɗin shiga sai talakawa. Yanzu kusan aji biyu ne wato ko dai masu kuka ko kuma waɗanda ba a ganin hawayen su. Shiri ne na gwamnati da ta riga ta ɗau matsaya da ba ja da baya sai dai wasu matakai na kawo sauƙi in har saukin ka iya samuwa. A kasa mai fiye da mutum miliyan 200 ai akwai babban ƙalubale na tsari da zai sa ko an ɓullo da wani shiri to wasu sai dai su ji a kafafen labaru. Yayin da shekarar ke ƙarewa mun ji an ɗan samu wani ragi na farashin man amma hakan ba zai yi tasirin da za a fahimta ba matuƙar litar da a watanni 5 na farkon bara ba ta kai Naira 200 a hukumance ba ta yi tsalle zuwa fiye da Naira 1000. Korafin jama’a ya sa shugaban ƙasa kan sa ya ce ya san zafin da mutane ke ciki amma nan gaba za a ga fa’idar hakan. Ba ma fidda tsammani daga rahamar Allah.

Wato idan ɗan boko ya yi magana bisa alƙaluman tattalin arziki da ya sani ‘yan uwa da ke jin jiki ba za su gane ba don ƙuncin ya yi yawa. Hausawa kan ce in duka ya yi yawa na ka kan kare. Yadda talakawa ke gane wani canji shi ne ta hanyar gani a tukunyar tuwon su. Idan gida ba a ɗora tukunya baa i ka ga duk wani bayani ba zai samu shiga da sauƙi ba. A gefe guda sai wannan batu na sabuwar dokar haraji da a ke damɓarwa a kan ta. Majalisa dai da alamu za ta fadada jin ra’ayin jama’a kan ƙudurin amma alamu na nuna ba za a fasa ba sai dai a samu ’yan gyare-gyare. Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce zai duba sabuwar dokar haraji da ya turawa majalisar dokoki.

Bola Ahmed Tinubu dai ya nuna lallai dokar na nan wato ma’ana ba zai fasa tsarin da ya ke nufin cimmawa ba.

Shugaban ya ce, ya na shirye da bitar dokar ko gyara wasu sassa da kuma sauraron ra’ayoyin jama’a.

In za a tuna sabuwar dokar ta tada kura musamman a arewacin Nijeriya kan harajin ɓAT da tunanin zai ƙara talauta yankin ne.

Matsin ya sa, shugabannin addini da na al’umma na kira ga neman taimakon Allah da gyara ɗabi’u don samun sauƙi. Shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ja hankalin jama’a wajen zama cikin masu gaskiya don hakan ne hanyar magabata.

Malamin na gabatar da wa’azi ne a garin Bauchi lokacin bitar ’yan agaji da a ka gudanar a jihar.

Malamin ya kawo misali da yanda Sahabbai su ka rayu cikin tsayawa kan gaskiya da tarihin ‘yan uwan Annabi Yusuf waɗanda a ka sanadiyyar karya da su ka yi a kan cewa kerkeci ya kashe Yusuf ya sa ko da lokacin da su ka fadi gaskiya kan tsare Bilyaminu a Misra mahaifin su Annabi Yakubu bai yarda da labarin su ba.

A nan Sheikh Bala Lau ya buƙaci kowa ya zama mai gaskiya kama daga ma’aikatan gwamnati, ’yan siyasa, ’yan kasuwa da sauran jama’a don samun rabauta a duniya da kiyama.

Malamin ya yi amfani da damar wajen kira ga shugaba Tinubu, ‘yan majalisar dokokin tarayya da gwamnoni su tuntuɓi jama’a yanda ya kamata kafin aiwatar da sabuwar dokar haraji.

Da alamu ɓangaren gwamnati zai sassauto kan wannan dokar aƙalla dai ko ta hnayar yi wa jama’a ƙarin bayani.

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ba shi da shirin rage yawan ma’aikatun gwamnatin sa don rage kashe kuɗin gwamnati.

Shugaban na magana ne a karo na farko da ya ke amsa tambayoyi a ganawa da manema labaru.

Gwamnatin Tinubu dai a yanzu ta na da fiye da ministoci 40 da ɗimbin masu ba da shawara da mataimaka.

Wannan dai bai zo daidai da umurnin shugaban kan rage adadin jami’an da ministocin za su riƙa tafiya da su a ciki da wajen Nijeriya ba.

Masana na ba da shawarar rage yawan masu mukamai a gwamnati a matsayin ɗaya daga matakan rage kashe maƙudan kuɗin gudanarwa.

Ba mamaki wani ya ce na kawo muhimman abubuwa biyu ne wato tsadar rayuwa da sabuwar dokar haraji ban kawo ɓangaren tsaro ba. Gaskiyar magana batun tsaro ba a wannan shekarar ya fara taɓarɓarewa ba. In mun tuna ai Boko Haram da ta yi sanadiyyar salwantar dubban rayuka ta faro ne tun 2009 a arewa maso gabar inda daga bisani kuma barayin shanu da su ka rikiɗe ɓarayin daji su ka ɓulla a arewa maso yamma. Tsageran Neja Delta sun yi sanyi tun matakan tsohon shugaba marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua yayin da a kudu maso gabar ba wani sabon abu ba ne ‘yan awaren Biyafara.

Kamar yanda a ka saba a duk shekara ranar 25 ga watan Disamba mabiya addinin Kirista na gudanar da bukin kirsimeti.

Tuni gwamnatin Nijeriya ta ba da hutun ma’aikata saboda wannan buki hakanan ma ta kara ba da wani hutun don sabuwar shekarar miladiyya ta 2025 mai shigowa.

Haƙiƙa an ga masu hannu da shuni a tsakanin mabiya addinin Kirista a Abuja na yanka manyan shanu don wannan ranar.

Zuwa yanzu dai ba wani labarin wani tashin hankali a faɗin Nijeriya kan wannan bukin inda wasu mabiya da dama su ka tafi garuruwan su na asali don wannan bukin.

Kazalika wasu musulmi ma a cikin ma’aikata a birane sun yi amfani da damar wajen yin tafiya da wasu hidimomin gaban su don hutun da a ka bayar.

Rundunar ’yan sanda ta cafke jagoran majami’a da muƙarrabai kan turereniyar da ta yi sanadiyyar asarar rayuka

Rundunar ’yan sanda ta Abuja ta cafke jagoran majami’a da muƙarrabai kan turmutsustsun da ya haddasa mutuwar mutum 10 a taron raba kayan tallafin abinci.

Akasin ya auku a harabar majam’ar katolika HOLY TRINITY ta anguwar Maitama a Abuja.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Abuja Josephine Adeh ta tabbatar da damƙe mutanen da zargin su da sakacin da ya kawo asarar rayuka ciki har ma da yara.

Nan take shugaban majami’ar katolika na Abuja Ignatious Kaigama ya yi tir da kama jami’an ya na mai kasa fahimtar dalilin yin hakan.

An samu irin wannan turereniyar a jihar Anambra da Oyo inda har shugaba Tinubu ya nuna damuwa da dora alhakin akasin kan waɗanda su ka shirya tarukan don sakaci da su ka yi.

Wani labarin kuma a bangaren masarutu in ka debe yanda ta ke kayawa a Kano tsakanin mai martba Sarki Aminu Ado Bayero da mai martaba Sarki Sunusi Lamido Sunusi sai labarin jihar Adamawa. Gwamnan jihar Adamawa Ahmad Fintiri ya ƙirƙiro karin masarautu 7 a jihar da ke arewa maso gabashin Nijeriya.

Kirƙiro masarautun ya biyo bayan amincewa da ƙudurin hakan da majalisar dokokin jihar ta yi inda gwamnan ya rantaba hannu a kai.

Wannan dai ya rage yawan ƙananan hukumomin babbar masarautar jihar ta Lamidon Adamawa daga 8 zuwa 4.

Hakanan matakin ya rage ƙananan hukumomin masarautar Mubi zuwa biyu daga biyar.

Gwamman ya ce ya ɗauki matakin don isar da gwamnati ga sassa, haɗin kai, sulhunta riciki da zaman lafiya.

Kammalawa;

Allah ya tabbatar ma na da alheri ya kuma sa mu shiga sabuwar shekarar 2025 cikin sa’a da samun saukin rayuwa. Ya dace kowa ya zauna shi kaɗai ya yi nazarin yanda zai inganta rayuwar sa da ta jama’ar da ke kewaye da shi ta hanyoyin ilimi da tuntuɓar juna wajen ayyukan gayya da haɗin kai. Nijeriya na bukatar yaki da ƙabilanci, ɓangaranci da rashin adalci bisa bambancin addini. In an samu maslaha kan waɗannan abubuwa 3 to ƙofar nasara da salama za ta buɗe da IKON ALLAH.

By ukarofi