Watanni bakwai bayan nasararsa ta farko, Oleksandr Usyk ɗan ƙasar Ukraine ya sake doke ɗan ƙƙsar Birtaniya Tyson Fury a ranar Asabar a birnin Riyadh, abin da ya sa ya ci gaba da riƙe matsayinsa bayan kare duka kambinsa na WBA da WBC da WBO.
Oleksandr Usyk ɗan ƙasar Ukrainian mai shekaru 37, ya nuna bajintarsa wajen taɓa Fury sau da yawa tare da doke shi da hannun hagu, abin da ya sa duka alƙalai ukun suka amince da ya samu maki 116-112, sannan ya ci gaba da zama ba’a yi nasara a kansa ba a fafatawar 23.
Da wannan nasarar yanzu ta kai Usyk fafatawa 23-0 ciki harda bugun ƙwab ɗaya 14, sannan ya ƙara darajar tagomashi da ya samu a rayuwarsa ta dambe baya ga zinare da ya samu a gasar Olympics a ajin masu nauyi.
Rashin nasarar ya sanya Fury mai shekaru 36 cikin rashin tabbas, inda yanzu yake 34-2-1, wanda ya sanar da yin ritaya a shekarar 2022 sai kuma ƙwasam ya canza ra’ayinsa ya koma filin daga.
Rahotanni sun ce jimlar kuɗin kyautar da aka ware a wannan karawar Riyad tsakanin Fury-Usyk ya kai dala miliyan 191, wato an samu banbancin kusan dala miliyan 56 fiye da fafatawarsu ta farko a farkon wannan shekarar, kuma wanda ya yi nasara shi ke da kashi 70 cikin 100 na ƙudin, sai kuma kashi 30 ga wanda aka doke.
