Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kungiyar Manoma ta ƙasa, reshen Jihar Katsina (AFAN) ta yaba wa Gwamna Dikko Radda bisa raba ma manoma tallafin kayan aikin gona mafi yawa a tarihin jihar Katsina.
Wata sanarwar ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar a jihar, RT Hon ya’u Umar Gwajo gwajo, ta ce tallafin kayan noman shine irinsa mafi girma a tarihin jihar Katsina.
Gwajo gwajo ya lissafa kayayyakin da aka raba wa manoma da suka haɗa da buhu 48.000 na takin zamani da injiunan huɗa guda 4,000 da famfuna na ban ruwa masu amfani da hasken rana guda 4,000 da kuɗin su ya ka Naira biliyan 8.
“A karon farko manbobin mu suka sami tallafi mai yawan gaske da zai inganta samar da abinci a musamman bayan kammala noman rana da ake aikin yanzu,” inji shugaban ƙungiyar.
Babu shakka acewarsa yawan takin zamani da gwamnati ta samar zai bunƙasa yawan amfanin da ake samu a kowacce kadada tare da kawar da matsalar samun taki a tsakanin manoma.
Gwamnatin jihar Katsina dai ta sayo kayan noman domin saidawa manoma akan farashi mai rangwame domin tallafawa manoma a faɗin jihar .
Shugaban ƙungiyar manoma wanda tsohon kakakin majalisar dokoki na jihar da a yanzu yake da riƙe da muƙamin mai baiwa Gwamna Shawara a kan harkan siyasa ya yi kira ga manoman da suka ci gajiyar tallafin da su guji sayar da su.
“Ku yi amfani da kayan wajan inganta noman ku, musamman noman rani da ake ciki yanzu.
