Babban Daraktan Cibiyar Rajin Kyautata Ayyukan Majalisar Dokoki da Yaƙi da Rashawa a Nijeriya (CISLAC), Kwamared Auwal Musa Rafsanjani, ya yi Allah-wadai da yanayin yunwa da fatara a Nijeriya, inda ya bayyana illar rashin shugabanci nagari da rashin ɗaukar matakan da suka dace na hauhawar farashin kaya.
Da yake mayar da martani game da mumunan turmutsitsin da ya laƙume rayuka da dama a faɗin ƙasar a yayin taron rabon abinci a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ƙarshen mako, Rafsanjani ya bayyana lamarin a matsayin abin da ke ratsa zuciya ga irin mawuyacin halin da ‘yan Nijeriya ke ciki.
“Wannan alama ce ƙarara cewa ‘yan Nijeriya na fuskantar mawuyacin hali a ƙarƙashin wannan gwamnati,” inji shi.
“Abin takaicin shi ne, gwamnati na ganin ta rabu da abubuwan da ke faruwa a ƙasa kuma ta kasa ɗaukar matakan da suka dace don magance lamuran da ke haddasa hauhawar farashi.
“Yayin da aka ba da rahoton waɗannan munanan al’amura, wasu da yawa na iya faruwa ba tare da an lura da su ba yayin da mutane ke tsananin yunwa.”
A Abuja, wani turmutsitsin da ya barke a yayin wani atisayen raba kayan abinci a cocin Holy Trinity Catholic Church da ke Maitama, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane goma, ciki har da yara hudu, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Taron wanda aka yi niyya don bayar da agaji ga marasa galihu, ya rikiɗe zuwa safiyar ranar Asabar, yayin da jama’a sama da dubu suka cika wurin.
