Gwamna Dauda ya amince da biyan kyautar albashi na wata ɗaya ga ma’aikatan Zamfara

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Gwamna Dauda Lawal ya amince da biyan albashin wata 13 ga ma’aikatan Jihar Zamfara

Sanarwar ta fito ne daga ofishin Shugaban Ma’aikata na Jihar Zamfara a cikin takardar da aka fitar a ranar 28 ga Disamba 2024.

Albashin wata 13 da aka amince da shi zai kasance na biyu a tarihin Jihar Zamfara, inda gwamnatin Lawal ta biya wannan albashi na farko a watan Disamba na shekarar da ta gabata.

Ma’aikatan gwamnati, ciki har da masu ritaya, za su samu ƙarin albashi na kashi 30 cikin 100 na albashinsu na asali a matsayin albashin wata 13. Wannan mataki na nuna godiya ga jajircewar ma’aikatan Jihar Zamfara da ƙoƙarin su wajen gudanar da ayyukan gwamnati, tare da ba su taimako na ƙarin kuɗaɗe a lokacin hutu. Wannan kuma yana cikin shirin gwamnati na ƙarfafa ma’aikata da tallafawa ci gaban tattalin arzikin Jihar Zamfara.

By ukarofi