Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, a ranar Talata ya bayyana damuwarsa kan wani sabon salon hada-hadar man fetur, inda ya ce ana amfani da yara da mata a matsayin garkuwar mutane a haramtattun matatun mai.
Gwamnan Bayelsa ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da sarakunan gargajiya da shugabannin ƙananan hukumomin jihar a gidan gwamnati da ke Yenagoa.
Ya ce, jami’an tsaro ne suka gano wannan mummunan lamari kan ayyukan leƙen asiri, ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya da su wayar da kan al’ummarsu illar harƙallar ba ta dace ba ga lafiyar ɗan Adam da muhalli.
Ya ce: “Rahoton da na samu kwanan nan shi ne, a wuraren da ake hada-hadar mai ba bisa ƙa’ida ba, yanzu suna da yara da mata, wanda hakan wani nau’i ne da ban taɓa gani ko ji ba.
“Wani lokaci, idan sojoji suka ba da izini su lalata waɗannan sansanonin kuma suka isa can don leken asiri, sai su gano cewa ana amfani da yara da mata don kare wuraren. Don haka ya zama dole mu haɗa kai a yankunanmu domin ilmantar da mutanenmu.
“Akwai wani yanayi da sojoji suka shiga suka gano cewa yara da mata suna can kuma dole su janye.”
Gwamna Diri ya buƙaci sarakuna da shugabannin kansiloli da su dauki matakin daƙile matsalar da ya ce ta faru a yankunan Kudancin Ijaw, Ekeremor, Brass da Nembe.
Ya kuma buƙaci sarakunan da su kai masa rahoton wuraren da ake tara mai a yankunansu, inda ya ƙara da cewa za a iya magance wannan mummunar ɗabi’a ta hanyar haɗin gwiwa.
