Turmutsutsun rabon tallafi: PDP ta buƙaci Tinubu ya sake duba manufofinsa na tattalin arziki

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Jam’iyyar PDP ta ce, turmutsutsun da aka samu a Nijeriya guda uku cikin ƙanƙanin lokaci ya nuna cewa akwai talauci da yunwa a ƙasar, wanda a cewarta yana da nasaba da irin mulkin Shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Kakakin PDP na ƙasa, Debo Ologunagba ne ya sanar da hakan a wata sanarwa, inda ya ce turmutsutsun da ake samu wajen rabon abinci abu ne da za a iya kiyaye afkuwarsu.

“PDP na baƙin ciki yadda gwamnatin APC te ɗaiɗaita tattalin arzikin ƙasar nan tare da jefa miliyoyin mutane cikin ƙangin talauci da yunwa, inda mutane da dama ba sa iya cin abinci, har wasu suke gwammace tafiya ƙasashen waje suna aiki masu wahala.

“Akwai takaici ganin duk da ɗimbin arzikin da Nijeriya ke da shi, ’yan ƙasar suna rayuwa cikin ƙunci, har ta kai suna mutuwa wajen karɓar abinci.

PDP ta kuma yi kira ga gwamnatin ta sake duba matakan da ta ɗauka da suka jawo tsadar rayuwa a ƙasar.

By ukarofi