Kotu ta umurci MTN ya biya kwastoma miliyan N15 kan cire kuɗi ba bisa ƙa’ida ba

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta umurci babban kamfanin sadarwa na MTN a Nijeriya da ya biya diyyar miliyan N15m bisa cire kuɗi daga asusun wani abokin kwastoma ba tare da izininsa ba.

Hakan ya biyo bayan shigar da ƙorafi da wani kwastoma, Ezugwu Anene ya yi inda ya ce an cire masa kuɗi kan sabis ɗin da bai yi rijista ba.

Wannan hukuncin ya fito ne daga kwamitin alƙalan kotun ɗaukaka ƙara mai mambobi uku, wanda Mai shari’a Okon Abang ya jagoranta.

Mai Shari’a, Abang ya karanto karar a ranar Juma’a 20 ga watan Disambar 2024 kan ƙorafe-ƙorafen.

Kotun ta bayyana cewa cire kuɗi daga asusun abokan hulɗa domin sabis na sabunta rajista ba tare da izini ba, haramun ne kuma ya zama wani nau’i na zamba.

Har ila yau, kotun ta ce aika saƙonnin kar-ta-kwana ba tare da izininsu ba ya saɓa wa haƙƙinsu na sirri da kuma ya saɓa ƙa’ida bisa tanadin Sashe na 37 na kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Kotun ta kuma jaddada cewa saƙonnin kar-ta-kwana marasa izini sun haifar da damuwa ga mai shigar da ƙara.

Ta ƙara da cewa, MTN na iya samun gagarumin riba daga wannan ɗabi’a, amma ’yan Nojeriya ba su sani ba.

Tun farko kotun ta jingine tarar N300,000 kan MTN inda mai ƙorafi ya ce an shafe shekaru ana cire masa N20 da zarar saƙo ya shigo wayarsa da sauran abubuwan da bai san da su ba.

Sai dai kamfanin MTN ya ƙalubalanci tarar inda ya ce kwata-kwata abin da ya cire daga layin Anene N14,000 ne.

By ukarofi