Al’ummar Zamfara na cikin haɗari kan faifan bidiyon Bello Turji – Dakta Shinkafi

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ya bayyana faifan bidiyo na baya-bayan nan da fitaccen ‘ɗan ta’addan nan Bello Turji ya fitar na mayar da garuruwa da ƙauyuka Kango a jihohin Sokoto da Zamfara a matsayin wani lamari mai tsanani dake buƙatar ɗaukar matakin gaggawa daga gwamnatin tarayya domin daƙile aniyar shi.

Dakta Shinkafi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau.

Jaridar Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa a ranar Larabar da ta gabata ne, fitaccen ɗan ta’adda Bello Turji ya fitar da wani faifan bidiyo da yayi kakkausan kalamai ga jami’an tsaro da su saki ɗan uwansa Bello Wurge da jami’an tsaro suka kama a kan gadon asibiti a babban asibitin Shinkafi.

Bello Turji a cikin faifan bidiyon ya yi barazanar ƙaddamar da hare-hare a garuruwa da ƙauyukan Shinkafi da Zurmi a Zamfara da kuma Isa a Jihar Sokoto.

Dakta Abdullahi Shinkafi ya koka da cewa, Turji a cikin faifan bidiyon ya yi alƙawarin dawo da garkuwa da mutanen yankunan Zamfara da Jihar Sokoto domin babu ƙaƙƙautawa.

Dakta Shinkafi, wanda tsohon sakataren jam’iyyar APGA ne na ƙasa kuma ɗan takarar gwamna a Jihar Zamfara ya bayyana barazanar Turji a matsayin bala’i wanda ya tayar da hankula a yankunan yayin da mazauna ƙauyukan suka fara yin Ƙaura zuwa wasu manyan garuruwa domin kare lafiyar su.

A cewarsa yanzu haka sama da ƙauyuka 48 da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Shinkafi sun zama ba kowa saboda fargabar sake ɓullowar hare-haren Bello Turji.

Ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki a jihohin Sokoto da Zamfara da su haɗa kai domin ganawa da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan lamarin domin sanya baki.

Ya buƙaci masu ruwa da tsaki a jihar kan buƙatar kafa kwamiti da nufin ganawa da shugaba Tinubu domin ɗaukar matakin gaggawa kan lamarin.

A cewar shi, Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, Gwamnonin jihohin Zamfara da Sokoto ya kamata su ɗauki matakin gaggawa akan ‘yan’taadda ƙarƙashin Bello Turji, yana mai cewar idan ba a yi haka ba, garuruwa da ƙauyuka da yawa za su zamo kango, domin Turji zai cika alƙawarin da ya yi.

Jigon na APC ya bayyana alhinin shi bisa yadda ake barin ’yan ta’adda suna yawo cikin walwala a yankunanan Shinkafi da Zurmi. Wannan a matsayin abun Kunya ga sojojin Najeriya.

Ya buƙaci sojoji da su ɗauki matakin da ya dace domin fatattakar ‘yan bindigar a yankunan.

Ya koka da cewa sama da kashi 85% na gonakin da ake nomawa a Zamfara ba a noma su a daminar bana saboda ayyukan ‘yan ta’addan a Jihar Zamfara.

“Abin takaici ne yadda sama da kashi 85% na gonaki ba a noma su a daminar da ta gabata a jihar Zamfara, don haka dole ne a gaggauta ɗaukar mataki domin daƙile waɗannan ‘yan ta’adda”. Yace

By ukarofi