

Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya rattaɓa hannu kan Kasafin kudin
shekarar 2025 dan inganta rayukan Al’ummar Jihar Kano.
Gwamna Abba Kabir ya ce wannan kasafin kuɗi zai taimaka matuka wajen cimma Muradun da za su kawo ma jihar Kano cigaba matuka dan samun saukin rayuwa ga musamman Al’umma matasa masu tasowa.
Haka kuma Gwamnan yana fatan wannan kasafin kuɗi zai ƙara bunƙasa hanyoyin samun damar bijiro da ayyuka kamar a bunƙasa harkokin Ilimi da Noma.
”Haka kuma muna fatan wannan Kasafin kudi zai taimaka wajen samar da Ayukan yi ga jama’ar Jihar Kano da Tallafawa harkokin Lafiya, Bada Jari da ga Matasa Maza da Mata.
Gwamman ya yaba wa Majalisar dokokin Kano bisa jagorancin Rt Hon Jibrin Isma’ila Falgore bisa ƙoƙarinsu bisa kwaskwarima wajen yadda kasafin ya samu kammaluwa.
”Yawan Kasafin kuɗin da ya tasar ma sama da bilyan N700 da za’a gudanar da ayyuka daban-daban wa Al’ummar jihar Kano.
Haka zalika ya ce manyan ayyukan raya ƙasa za su laƙume sama da naira bilyan N400 da za su inganta ayyukan ci-gaba a jihar.
Bilyan N29 kuma, za a cigaba da juyawa a wannan sabuwar shekara don samar da aikin cigaba,sannan akwai kudaden da muke sanya ran samun sama da naira bilyan dari biyar daga gwamnatin Tarayya dama wadanda zasu rinka shigowa daban-daban.
Gwamnan Kanon ya kuma muka sakon godiyarsa ga ɗaukacin jama’ar jihar bisa dukkan Addu’o’in da suke yi masa.
