Gwamnatin Australia ta gargaɗi ‘yan ƙasarta kan shigo wa Nijeriya

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Gwamnatin Australia ta fitar da wata sanarwa mai tsauri, tana gargaɗin ‘yan ƙasar su sake tunanin buƙatar yin tafiya zuwa Nijeriya. Ma’aikatar harkokin waje da ciniki ta Australia (DFAT) ce ta bayar da wannan gargaɗin ranar Talata, inda ta bayyana matsalar tsaro mai tayar da hankali da ta haɗa da ta’addanci, garkuwa da mutane, da kuma yiwuwar rikicin farar hula a matsayin dalilan wannan shawara.

A cikin sanarwar, gwamnati ta ce: “Ku sake tunanin buƙatar tafiya zuwa Nijeriya gaba ɗaya saboda yanayin tsaro mara tabbas da barazanar ta’addanci, garkuwa da mutane, laifuka masu tsanani, da kuma yiwuwar rikicin farar hula. Akwai babban hatsarin hare-haren ta’addanci daga ƙungiyoyi daban-daban.

Hare-haren na iya faruwa ba tare da tsammani ba ko kuma su auna abubuwan da suka shafi ƙasashen waje.”

Sanarwar ta ƙara jaddada cewa wuraren da jama’a ke taruwa na iya zama abin hari, ciki har da otal-otal, mashaya, gidajen abinci, tarukan siyasa, gine-ginen gwamnati, wuraren ibada, makarantu, kasuwanni, wuraren cin kasuwa, tarukan wasanni, tashoshin sufuri, cibiyoyin tsaro, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da kuma sansanonin ‘yan gudun hijira.

Hakazalika, an yi gargaɗin musamman ga jihohin Adamawa, Anambra, Akwa Ibom, Bauchi, Bayelsa, Borno, Kuros Ribas, Delta, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Neja, Filato, Ribas, Sakkwato, Taraba, Yobe da Zamfara.

Sanarwar ta kuma yi nuni da alƙaluman hukumar ƙididdiga ta Nijeriya (NBS) da suka nuna cewa an samu mutum 2,235,954 da aka yi garkuwa da su tsakanin Mayu 2023 zuwa Afrilu 2024. Adadin kuɗaɗen fansa da aka biya a wannan lokacin ya kai kimanin naira tiriliyan 2.2, inda aka biya matsakaicin naira miliyan 2.7 a kowanne hari.

Yankin Arewa maso Yamma ya fi yawan a adadin kuɗaɗen fansa da aka biya, wanda ya kai naira tiriliyan 1.2, yayin da yankin Kudu maso Gabas ya fi ƙarancin adadi, inda aka biya naira biliyan 85.4. Wannan matsalar tsaro mai tsanani ta sa Australia ta ƙara jaddada gargaɗin ta kan tafiye-tafiye zuwa Nijeriya ga ‘yan ƙasar.

By ukarofi