Da kafafen sada zumunta ana iya gina ƙasa a kuma bunƙasa arziki – Yusha’u Shuaibu

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano 

Gidauniyar Adnan Mukhtar and Associates ta shirya taron lakca don taya murnar ranar haihuwa ga Shugaban rukunin makarantu MAAUN Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, da ya cika shekara 47 a duniya a gidan Mumbayya Gwammja, Kano ranar Litinin.

A  jawabinsa, ƙwararen masani akan kafofin yaɗa labarai kuma masani akan kafafen sadarwa na zamani, kuma shugaban Kamfanin PRNigeria Alhaji Yusha’u Shuaibu ya bayyana cewa muhimmancin soshiyar midiya wajen gidlna ƙasa, inda ya ce “Mutane da yawa suna soshiyal midiya amma sun fi amfani da ita ne ta hanyar raha wato entertainment abinda muke cewa shi ne za mu iya amfani da ita wajen bunƙasa arzikin ƙasa kuma su taimakawa kansu, misali kana da wani sana’a da ka ke yi sai ka yi amfani da wannan kafa ta soshiyal midiya ka tallata abinda kake sayarwa,”

Ana amfani da wannan kafa ta hanyoyi daban-daban akwai kuma hanyar da ake amfani da ita ta hanyar da ba ta dace ba, shi ne hanyar farfaganda ƙaryace-ƙaryace, akwai wacce ake yin ta da gangan don a bata wani ko don a sa mutane su ji haushi su tunzura su yi abinda bai dace ba.

“A taƙaice za ka cewa akwai amfani da rashin amfani na sociyal midiya kuma muka gaya masu yadda zaa yi amfani da ita ta hanya mai kyau da kuma cigaban kasa,” inji Malam Yusha’u Shuaibu.

Adnan Mukhtar shi ne shuganan Gidauniyar ya bayyana cewa sun shirya lakca ne akan yadda za a yi amfani da social media wajen gina kasa da kuma yadda zaa yi amfani da ita ta hanyar da ta dace.

“Maimakon aiwatar da taruka da  bukukuwa na tunawa da ranar haihuwarsa, shi ya sa muka ga ya dace mu shirya lakca da za ta amfani al’ummar wannan zamani.” 

Adnan ya ƙara da cewa: “A matsayinmu na masoya Farfesa Adamu Gwarzo muka ga ya dace mu zo da sabon tsari domin matasanmu su amfana a samu iliimi wannan ya fi muhimmanci akan duk wani abu da za a yi.

“Mun ƙaru da hanyoyin da za mu gina ƙasa mu kuma kawo wa kanmu da kanmu ci gaba.”

Farfesa Adamun Abubakar Gwarzo shi ne mu’assasi kuma shugaban Jami’ar Maryam Abacha da Jami’ar France-British International Kaduna da kuma Jami’ar Canadian ta Nigeriya, Abuja 

Taron ya samu halartar wakilin Farfesa Adamu Gwarzo Farfesa Muhammad Isar da Dr. Sule Ya’u Sule da ya zama Shugaban taro da da sauran masana da matasa maza da mata da ke faɗin ƙasar nan.

By ukarofi