Rikicin APC a Zamfara: Shinkafi ya rubuta wa Tinubu da Ganduje wasiƙa

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jigo a jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a Jihar Zamfara Dr Sani Abdullahi Shinkafi ya rubutawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa Abdullahi Umar Ganduje wasiƙa kan halin rikicin dake neman kunno Kai a jam’iyyar ta APC na yunƙurin ɗora ‘yan takara a zaɓen 2027, inda ya bayyana cewar hakan ba zai ƙara yin aiki a jihar ba.

Dakta Shinkafi wanda ya bayyana cewar ya tsallake rijiya da baya a wani yunƙurin hallaka shi a ranar Juma’ar da ta gabata da wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne suka yi masa biyo bayan sukar da ya yi a kwanan baya na yunƙurin ɗora ‘yan takarar jam’iyyar, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya yi gaggawar ceto jam’iyyar APC, da jihar daga rashin tsaro tun kafin lokaci ya ƙure.

Jigon na jam’iyyar APC wanda ke magana da manema labarai a daren Asabar a Gusau, babban birnin jihar, ya bayyana cewa an kai masa hari a masallacin Juma’a na Rabi’atu a lokacin da ya halarci wani ɗaurin aure a Gusau.

“Mummunan halin da jam’iyyar APC ke ciki a jihar Zamfara yana da matukar muni kuma ya kamata shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da shugaban jam’iyyar mu ta ƙasa Abdullahi Ganduje su yi gaggawar ceto jam’iyyar APC ta Zamfara kafin lokaci ya ƙure”.

Dakta Sani Shinkafi ya koka da cewa waɗanda ake zargi da yunƙurin kashe shi ‘ya’yan jam’iyyar sa ne, (APC) wanda ya bayyana a matsayin da gangan aka yi yunƙurin hallaka shi bisa kiran da ya yi na a yi wa APC da jama’ar jihar adalci a kwanakin baya.

“Na gane waɗanda suka kai min hari dukkanin su ‘yan APC ne, kuma wannan manufa ce ta daƙile ni, domin na fito fili na soki ɗauki ɗoran ‘yan takara gabanin babban zaɓen 2027 da kuma yadda aka kasa kama Ƙasurgumin ɗan ta’adda Bello Turji.” Ya ce.

“Duk mun ga yadda APC ta yi rashin nasara a Zamfara a 2019 da 2023 saboda sanya ‘yan takara kuma hakan ba zai sake faruwa ba”.

“Babu wanda zai hana ni yin magana, zan ci gaba da bayyana ra’ayi na wajen yaƙi da ɗora ‘yan takara, zan ci gaba da zama a APC, mu yaƙi zalunci.”

Ya kuma yi kira ga gwamna Dauda Lawal da yayi gaggawar dakatar da ayyukan ‘yan bangar siyasa a jihar.

Hakazalika, jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta yi Allah-wadai da harin da wasu ‘yan barandan jam’iyyar APC suka kai wa Dakta Sani Abdullahi Shinkafi a jihar.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na jihar, Yusuf Idris a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ya bayyana harin a matsayin wanda ba za a amince da shi ba.

“Jam’iyyar APC gaba ɗaya ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa Sani Abdullahi Shinkafi yayin ɗaurin auren ‘ya’yan Alhaji Siddi Ɗaki Takwas, irin wannan ɗabi’a ya saɓawa kimar jam’iyyarmu,” inji shi

“Jam’iyyar za ta ɗauki dukkan matakan da suka dace don ganin an kama masu aikata irin wannan rashin ɗa’a tare da hukunta su kamar yadda doka ta tanada,” in ji shi.

By ukarofi