‘Yan sanda sun ceto jaririn da aka jefar, sun kama mahaifiyarsa a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar ƴan sanda a Abuja a ta yi nasarar ceto wani jariri ɗan kwana ɗaya da haihuwa a kusa da wani juji dake bayan wata kasuwa da aka jingine aikinta a yankin Mpape dake birnin.

Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta faɗi hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi inda ta bayyana wa al’umma yadda aka ceto jaririn.

Ta ce a safiyar ranar 3 ga watan Junairu ne jami’an rundunar na Mpape suka samu rahoto game da jaririn inda bayan sun garzaya ne sai suka same shi a ƙunshe cikin zani.

SP Josephine ta ce tuni aka kai shi wani asibitin gwamnati dake yankin inda aka tabbatar da lafiyarsa.

A lokacin da aka gudanar da bincike a yankin, an yi nasarar kama mahaifiyarsa mai suna Khadija Ali inda ta tabbatar da cewa jaririn nata ne.

Ta ce ta yi hakan ne sakamakon ba ta da ƙarfin kula da shi bayan tserewa da mahaifinsa ya yi.

Saidai, rundunar ƴan sandan ta yi alla-wadai da ɗanyen aikin tare da tabbatar wa al’umma ƙoƙarinsu na cigaba da bai wa marasa galihu kariya acikin al’umma.

Sanarwar ta ƙara da cewa, za a miƙa jaririn ga ɓangare kula da walwala don samun kulawar da ta dace, yayin da kuma za a cigaba da bincike akan mahaifiyar.

Kazalika, rundunar ta yi kira ga al’umma da ta cigaba da ba ta haɗin kai da sanya ido akan abubuwan da suke faruwa a yankunansu tare da aiko musu da rahoton duk wani abin zargi ta lambobi kamar haka; 08061581938, 08032003913, 08028940883, CRU: 08107314192, PCB: 09022222352.

By ukarofi