Nijeriya za ta taimaka wa Ghana – Tinubu ga sabon shugaban ƙasar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya Shugaba John Mahama na Ghana bisa rantsar da shi da aka yi, ya na mai cewa Nijeriya za ta taimaka wa ƙasar ta hanyoyin da suka dace.

A ranar Talata ne aka rantsar da Mahama a matsayin shugaban ƙasar bayan shekaru da dama da ya jagoranci ƙasar a baya.

Shugaba Tinubu yana ɗaya daga cikin shugabannin da suka halarci taron rantsarwar, ya na mai jaddada ƙarfin abota da alaƙar dake tsakaninsa da Mahama da kuma ƙasarsa ta Ghana.

A shekarun 2012 zuwa 2017 ne Mahama ya shugabanci Ghana bayan nasara da ya samu akan abokin karawarsa, Mahamudu Bamuwiya a babban zaɓen ƙasar.

Tinubu ya bayyana Shugaban ƙasar a matsayin jagora mai kishi da hangen nesa wanda ake sa ran zai kai ƙasar ga cimma nasarorin ci-gaba.

Ya kuma yi masa addu’ar samun nasara a shugabancin nasa domin amfanin al’ummar ƙasar da ma shiyyar Afirka ta Yamma baki ɗaya.

By ukarofi