ICPC ta maka tsohon hadimin El-Rufa’i kotu bisa zargin almundahana

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar ICPC ta gurfanar da tsohon shugaban ma’aikatan tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, Alhaji Muhammad Bashir Saidu, a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna. Haka kuma an gurfanar da wani jami’i a ma’aikatar kuɗi, Ibrahim Muktar, bisa tuhumar da suka shafi zargin almundahana da karkatar da kuɗaɗe.

Bisa ga tuhumar da ake yi ƙarƙashin lamba FHC/KD/IC/2025, ana zargin Bashir Saidu, wanda ya taɓa zama Kwamishinan Kudi na Kaduna, da karɓar kuɗaɗe da suka haura Naira miliyan 155 a watan Maris na shekarar 2022, ta hannun wani hadiminsa mai suna Muazu Abdu.

Hukumar ICPC ta bayyana cewa kuɗaɗen sun kasance na wata haramtacciyar hanya kuma hakan ya saɓa wa dokar kuɗaɗe ta shekarar 2022.

A cewar dokar kuɗaɗe ta 2022, duk wanda aka samu da laifin irin wannan yana iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekaru huɗu zuwa 14, ko tara daidai da sau biyar na kuɗin da aka samu daga laifin, ko ma a haɗa duka biyun. Tuhumar da ake yi wa Saidu da abokin zamansa an gabatar da ita ne a ranar Talata, 7 ga Janairu, 2025, ta hannun lauyan hukumar ICPC, Dakta Osuobeni Ekoi Akponimisingha.

Kotun ta shirya sauraron ƙarar a ranar da za ta bayyana, inda ake sa ran za a ci gaba da bayyana gaskiyar zarge-zargen da ake yi wa waɗanda ake ƙara. Wannan na zuwa ne bayan dogon bincike da aka yi kan zargin almundahana da ya shafi tsohon kwamishinan.

By ukarofi