NFF ta naɗa kocin Super Eagles na dindindin

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta amince da naɗin Éric Sékou Chelle a matsayin sabon kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya, Super Eagles. Wannan naɗin ya biyo bayan shawarar kwamitin da ke da alhakin zaɓen kocin ya bayar, wanda ya gabatar da sunan Chelle a taron da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, 2 ga Janairu, 2025.

Chelle, wanda ya taɓa horar da tawagar ƙwallon ƙafa ta Mali tun daga 2022, ya taka rawar gani a gasar cin kofin Afrika na 2023 da aka gudanar a Cote d’Ivoire, inda tawagarsa ta kusa kai wa matakin kusa da na ƙarshe. Duk da haka, Mali ta sha kashi a hannun ƙasar mai masaukin baƙi, Cote d’Ivoire, da ci 2-1 a ƙarin lokaci, bayan sun jagoranci wasan har zuwa minti na ƙarshe.

A matsayin ɗan wasa, Chelle mai shekaru 47 ya wakilci ƙungiyoyi daban-daban a Faransa, ciki har da Martigues, Valenciennes, Lens, Istres, da Chamois Niortais. A matsayin koci, ya horar da ƙungiyoyi irin su GS Consolat, FC Martigues, Boulogne, da MC Oran kafin ya zama kocin tawagar Mali.

Hukumar NFF ta bayyana cewa naɗin Chelle zai fara aiki nan take, tare da burin jagorantar Super Eagles don samun gurbi a gasar cin kofin duniya na FIFA da za a gudanar a 2026. Wasannin share fagen gasar da za su gudana a watan Maris, inda ake sa ran kocin zai fara aiki da ƙarfin gaske don ganin tawagar ta samu nasara.

By ukarofi