Jami’an tsaro sun kashe mutum biyu da ake zargin su da kisan sojoji huɗu a Ribas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar sojojin ƙasa ta ce jami’anta sun harbe wasu mutane biyu da ake zargin su da hannu a kashe wasu sojoji huɗu da ke bakin aiki a Jihar Ribas.

Kakakin dakarun sojojin rukuni na 6 dake Fatakwal, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce jami’ansu na Bataliya ta 5 sun yi nasarar cimma waɗanda ake zargin ne a maɓoyarsu dake Kalaogbokolo, a ƙaramar hukumar Ahoada ta Yamma dake jihar.

Ya ce a ranar 12 ga watan Disamba, 2023 ne ƴan ta’addar suka hallaka sojoji huɗu tare da yin garkuwa da wasu ƴan ƙasar Koriya da ke yi wa kamfanin Daewoo Nigeria Limited aiki.

An kama biyu daga cikin ƴan ta’addar ne yayin da aka harbe su a lokacin da suka yi yunƙurin tserewa bayan farautarsu da sojojin suka yi, inji kakakin.

Jami’an tsaron sun kuma yi nasarar ƙwato makamai daga hannun ƴan bindigar da suka haɗa da bindiga ƙirar AK47 da mujallunta guda uku da alburusai uku na 7.6mm da guda 13 na 7.6mm NATO.

Rundunar ta ƙara da cewa jami’anta za su cigaba da zaƙulowa da hukunta waɗanda ke da hannu a ire-iren waɗannan manyan laifuka da ƙoƙarin bai wa rayuka da dukiyoyin al’umma kariya.

By ukarofi