Manyan muƙarraban Tinubu sun fi na Buhari haɗari – Solomon Dalung 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Solomon Dalung, tsohon ministan matasa da wasanni, ya ce muƙarraban da ke kewaye da Shugaba Bola Tinubu sun  fi na tsohon Shugaba Muhammadu Buhari haɗari, wayewa, da burin cimma manufofi.

Blueprint ta rawaito cewa a yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels a ranar Talata, Dalung, wanda a baya ya bayyana cewa akwai wasu mutane da ke tafiyar da gwamnatin Buhari a ɓoye, ya ce waɗanda ke kusa da Tinubu sun fi haɗari.

Ya ƙara da cewa muƙarraban dake kewaye da Buhari ba su da ilimi sosai kuma ba su da gogewa a fannin siyasa da mulki, yayin da waɗanda ke kusa da Tinubu suka kasance masu wayewa, burin cimma nasara, da ilimin dabarun mulki.

“Tabbas, gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari tana da masu juyata a ɓoye. Wannan abu ne da aka sani, kuma na shaida hakan. Sai dai basu da wayewa da gogewa ta sanin siyasa da rayuwa.

“Tinubu kuwa ya kewaye kan sa da mutane da suka goge da rayuwa suka waye kuma su ka laƙanci siyasa. Dole su fi haɗari kuma fadar shugaban ƙasa za ta ji a jikin ta saboda mutane ne da suke da basirar da za su kange shugaban ƙasa su hana kowa raɓar sa da mai kai masa bayanai,” inji shi.

By ukarofi