China ta ware Dala miliyan 255 domin kammala aikin jirgin ƙasan Kano-Kaduna

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Bankin ƙasar China ya amince da bayar da Dala miliyan 254.76 domin kammala aikin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Kaduna.

Bankin ya amince ya ba da rancen ne gabanin ziyarar da Ministan Harkokin Wajen China, Mista Wang Yi, zai kawo Nijeriya a wannan makon, inda ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba.

Aikin titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Kaduna mai nisan kilomita 203 zai ci kuɗi Dala miliyan 973, kuma zai sada su da Abuja.

Aikin ya samu tsaiko amma Bankin na a China ya ba da tabbacin samar da isassun kuɗaɗe domin tabbatar da kammalawa cikin lokaci.

Ana sa ran sufurin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Abuja sai sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da harkokin kasuwanci tsakanin sauran sassan Nijeriya da Kano, cibiyar kasuwanci.

By ukarofi