Daga BELLO A. BABAJI
Shugaban jam’iyyar SDP na ƙasa, Shehu Gabam ya fitar da jawabin da suka tattauna da jigo a jam’iyya mai mulki ta APC, Malam Nasiru El-Rufa’i.
Gabam ya gabatar da hakan ne a yayin hira da gidan talabijin na ‘channels’ a ranar Alhamis inda ya ce babu laifi acikin tattaunawa da jami’yyarsa ta yi da tsohon gwamnan Kaduna, El-Rufa’i.
Ya ce, “Mai ya sa ake damuwa game da tattaunawa da tsohon gwamnan da Segun Sowunmi” da aka ce ba su da muhimmanci, inda ya ƙalubalanci rashin ba su muƙaman da suka nema na inganta harkokin gwamnati.
Jagoran jam’iyyar ya ce sun gana ne akan abin da ya shafi nazari game da halin da ƙasar ta tsinci kanta a shekarar 2024, inda ya ce a matsayin jami’yyarsu ta adawa da ke da wakilai a matakai na ƙasa, na jihohi da ma a ƙananan hukumomi, akwai buƙatar su buɗe ƙofa ga mutane da dama a lokacin da suka ga abubuwa ba sa tafiya daidai.
Ya ƙara da cewa haka APC ta yi a lokacin da ta ga PDP ta gaza inda ta tara mambobi daga ɓangarori da dama, ta yi maja tare da da lallasa ta.
SDP ta hannun shugaban nata ta ce ba sabon abu bane kiran ganawa da El-Rufa’i ko wani ɗan siyasa da har zai haifar da kumfar baki.
Ya kuma yi tsokaci game da halin matsin da al’umma suke ciki a Nijeriya, ya na mai cewa ƙasar ba ta taba samun kanta a irin haka ba, kuma ministocin Shugaban ƙasa ba su da ikon sauya tsarin da ya ke tafiya akai wajen gudanar da mulki.
