Nijeriya ta bukaci MDD ta binciki yadda Boko Haram ke samun kuɗaɗe da horo

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Najeriya ta yi kira ga Majalisar ɗinkin Duniya da ta gudanar da bincike kan yadda ake samar da  kudade da horar da ‘yan ta’addan Boko Haram.

Blueprint ta rawaito cewa Babban Hafsan Tsaro na ƙasar, Janar Christopher Musa, ne ya yi wannan kiran a wata hira da ya yi da Al-Jazeera kwanan nan.

Musa ya bayyana cewa akwai wata hanyar samun kudade ta duniya ga ‘yan ta’addan, inda ya jaddada bukatar Majalisar dinkin duniya ta shiga don gano asalin kudaden.

Janar din ya tambayi yadda ‘yan ta’addan su ka samu damar tsayawa tsawon shekaru 15 suna ci gaba da kai hare-hare, tare da zargin haɗin baki da ƙasashen duniya wajen ba su kuɗaɗe, horo, da kayan yaƙi.

Da ya ke mayar da martani kan tambayar dalilin da ya sa Boko Haram ke ci gaba da sake kara karfi duk da iƙirarin gwamnatin tarayya cewa an rage musu karfi,  ya ce: “Matsalar ita ce, na yi tunanin mun yi magana da al’ummar duniya. Mu gano asalin kuɗaɗen. A halin yanzu, sama da mambobi 120,000 na Boko Haram sun mika wuya, kuma mafi yawansu sun zo da kuɗaɗe masu yawa. Yaya suka same su? Ta yaya ake samun kuɗaɗen? Yaya aka horar da su? Yaya suka samu kayan aiki?

“Akwai buƙatar shiga cikin wannan lamari domin mu gano inda kuɗaɗen suka fito. Wani al’amari ne na ƙasa da ƙasa, kuma ba mu da ikon sarrafa shi,” inji shi.

By ukarofi