Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kalaman da gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammad, ya yi wa fitaccen malamin addini Sheikh Yahaya Jingir game da mawuyacin halin da ake ciki a Nijeriya na ci gaba da jan hankalin jama’a musamman a shafukan sada zumunci.
Cikin wani bidiyon da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an ga Gwamnan Bala Mohammed, na jawabi ga Sheikh Jingir a fadar gwamnatin Bauchi lokacin da shehin malamin ya kai masa ziyarar ta’aziyar rashin matar mahaifinsa.
An jiyo gwamnan na shaida wa Sheikh Jingir cewa ya kamata ya faɗa wa Shugaban ƙasa Bola Tinubu halin da ƙasar ke ciki sakamakon wasu manufofin gwamnatinsa.
”Kai ka bambanta ƙwarai da sauran malamai da ke goyon bayan gwamnatin Muslim-Muslim, saboda kai kowa naka ne, kuma Allah ya sa har yanzu kana da rai, kuma kana faɗa ana ji,” inji gwamnan.
”Watakila ka ji wasu maganganu tsakaninmu da Tinubu, to da gaske ba mu shiri da shi.”
Gwamnan ya zargi Tinubu da ma gwamnoni da jefa ‘yan Nijeriya cikin mawuyacin halin matsin tattalin raziki.
A cewarsa: ”Sakamakon abubuwan da ya kawo wanda ba shi sauraron mutane, ba shi ji ba shi gani, abin kamar zai halaka mu mu al’ummar arewacin Nijeriya.”
Bala Mohammed ya bayar da misali da batun ƙudirin haraji da Shugaba Tinubu ya gabatar wa majalisar dokokin ƙasar, wanda ke buƙatar aiwatar da wasu sauye-sauye kan yadda ake karɓa da kasafta harajin.
Gwamnan ya ce da kuɗin haraji ne gwamnatocin jihohi ke samun kuɗaɗen aiwatar da ayyukansu.
Gwamnan da ake yi wa laƙabi da Kauran Bauchi, na daga cikin gwamnonin arewacin ƙasar da suka fito fili ƙarara suka yi adawa da sabon ƙudirin harajin da ake son sauya wa fasali.
Bala Mohammed ya ce dama yana da niyyar zuwa har gidan Sheikh Jingir domin sanar da shi matsayarsa kan matakin na shugaban ƙasa.
”Watakila kana cikin mutaten da suke yi wa shugaban ƙasa magana kuma ya saurare su… muna so a faɗa wa shugaban ƙasa cewa ƙudurorin da yake gudanarwa ba su aiki”, a cewar gwamnan na jihar Bauchi.
Tun da farko a jawabinsa, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce jagoranci na buƙatar jajircewa.
Ya ce a lokacin da Allah ya aiko Annabi Nuhu sai da ya shekara 950 yana wa’azi amma bai samu mabiya da suka kai 100 ba. Amma duk da haka Annabin bai yi ƙasa a gwiwa ba.
”Shi ya sa ni ma nake wahala da Muslim-Muslim [gwamnatin Tinubu da Shettima], saboda kafin abin ya shiga ƙwaƙwalwar mutane da wahala,” inji malamin.
Sheikh Jingir na cikin manyan malaman Musulunci da ke goyon bayan gwamnatin Tinubu ta ”Muslim-Muslim” – wato shugaban ƙasa da mataimakinsa duka mabiya addinin Musulunci.
An sha jin malamin na kare manufofin gwamnatin Tinubu a wuraren wa’azi a lokuta da dama, abin da ya janyo masa suka daga wasu ‘yan ƙasar da ke ganin baiken gwamnatin Tinubun.
