Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da wani masallaci a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na Jihar Katsina ya buƙaci masu hannu da shuni da su gina masallatai da makarantun Islamiyya waɗanda za su taimaka wajen tarbiyyartar da al’umma.

Ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake ƙaddamar da wani sabon masallacin Juma’a a ƙaramar hukumar Sandamu, wanda wani jami’in “yan sanda, AIG Mustafa Bala Sandamu, ya gina.

Gwamna Raɗɗa ya ce gina masallatai da makarantun islamiyya zai taimaka matuƙa wajen koyar da ilimi da kyawawan halaye wanda zai sa al’umma ta inganta.

Ya umurci kwamitin masallacin da al’ummar garin Sandamu da su riƙa ba masallacin irin kulan da ya dace tare da yin amfani da shi a matsayin cibiyar koyo da inganta tarbiyya.

A nasa jawabin, mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, ya miƙa godiyar sa a madadin al’ummar Sandamu da masarautar Daura ga wanda gina masallacin.

Sarkin ya kuma ƙaddamar da limami da mataimakin limamin masallacin da sauran ‘yan kwamitin masallacin tare da horarsu da kula da masallacin da yin wa’azi da tarbiyya ga al’uma.

Tun da farko a cikin huɗubarsa ta Juma’a, limamin masallacin, Sheikh Abdulhadi Aliyu Daura, ya bayyana gina masallaci a matsayin ɗaya daga cikin ayyukan ibada da ke da ɗimbin lada a wurin Allah Maɗaukakin Sarki.

Ya kuma buƙaci al’ummar musulmi da su ci gaba da yi wa shugabannin ƙasar nan a kowane mataki addu’a domin samun nasara wajen inganta walwala da jin daɗin ‘yan ƙasa.

Taron ƙaddamar da masallacin ya samu halartar manyan jami’ai da suka haɗa da mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Alhaji Bala Abu Musawa, da ‘yan majalisar zartarwa na jihar Katsina da hakimai a masarautar Daura.

By ukarofi