Daga BELLO A. BABAJI
An zaɓi Sanata John Azuta-Mbata a matsayin shugaban ƴan ƙabilar Igbo na Duniya baki ɗaya.
Azuta-Mbata shi ne tsohon Sanatan Ribas ta Gabas a Majalisar Tarayya, wanda aka zaɓe shi a tsohon masaukin gwamnatin jihar Enugu dake Enugu, babban birnin jihar bayan ganawa da masu-ruwa-da-tsaki.
Taron ya samu halarcin wakilai daga Kudu maso Gabas inda aka samu kimanin wakilan ƙungiyoyi 200.
Mbata zai gaji Ozichukwu Chukwu a muƙamin wanda ɗan jihar Imo ne.
An haifi Mbata ne a Junairun shekarar 1960 inda ya yi karatun digirinsa na biyu a Jami’ar Ibadan.
Ya kuma taɓa zama Sanata daga shekarar 1999 zuwa 2003 a ƙarƙashin jami’yyar PDP.
Haka kuma ya taɓa zama ɗaya daga cikin mambobin Majalisar Zartarwa ta Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Fatakwal.
