Daga BELLO A. BABAJI
Wata kotu a Amurka ta yanke wa zaɓaɓɓen Shugaban ƙasar, Donald Trump hukunci kwanaki goma gabannin rantsar da shi, bayan samun sa da hannun a biyan wasu kuɗaɗen ayyukan masha’a ga wata tauraruwar finafinan batsa, Stormy Daniels.
Hukuncin ya nuna cewa babu wani kuɗi da Trump zai biya a matsayin tara ko kuma zuwa gidan yari ko yiwuwar tuɓe shi daga kujerarsa.
Alƙali Juan Merchan ya yi hukuncin wanda hakan ya kawo ƙarshen tsawon shekara guda da aka ɗauka ana jinkirtawa, ya na mai bayyana hakan a matsayin abin da ba a saba gani ba.
Tun a watan Maris, 2023 ne aka sanya Shugaba Trump cikin waɗanda ake tuhuma da hannu a biyan Daniels wasu kuɗaɗe da adadinsu ya kai Dala 130,000 a shekarar 2016.
Haka ma a ranar 30 ga watan Mayu na 2024 ne aka samu Trump da hannu dumu-dumu a laifuka 34 na ƙaryata kundaddakin kasuwanci.
Saidai biyan irin waɗannan kuɗaɗen ba haramun bane a New York amma hanyar da ya bi na sanya lauyansa wanda ya biya kuɗin shi ya haifar da zargin akan sa.
