An ƙaddamar da makaranta da masallaci na waƙafi na Marigayi Aminu Maifamfo

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMAD a Kano

Mataimakin Gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya jagoranci ƙaddamar da buɗe makaranta da masallaci ta gidauniyar waƙafi ta da khumusi ta Marigayi Aminu Umar Mai famfo da ɗan sa mataimakin manajan daraktan Hukumar KASCO, Hon. Aminu Aminu ya gyara aka ƙaddamar a Unguwar Kawaji.

Mataimakin Gwamnan Kwamred Aminu Gwarzo ya yaba wa iyalan Marigayin bisa cika wannan buri na mahaifinsu na samar da makarantar da masallaci ya bayyana Marigayi Aminu Umar Maifamfo da dattijon arziƙi da ya bada gudunmuwa a rayuwarsa wajen tallafawa al’umma kuma Allah ya albarkaci bayansa cikin zuri’arsa aka samu gwani na ƙur’ani.

Kwamred Aminu Abdussalam wanda kuma shine Kwamishinan ma’aikatar Ilimi mai zurfi na jihar Kano ya bayyana goyon bayan Gwamnatin Jihar Kano ga makarantar da bata kulawa yadda za ta amfani al’ummar Kawaji da ƙaramar hukumar Nasarawa dama jihar Kano tare da kira ga al’ummar yankin su yi amfani da makarantar wajen ilmantar da ɓaɓansu.

Da yake zantawa da ‘yan jarida bayan ƙaddamar da buɗe makarantar, Hon. Aminu Aminu Maifamfo ya ce dama makarantar da masallacin harsashi ne da mahaifinsa ya dasa bayan  rasuwarsa cikin ikon Allah bayan shekara 20 ya tabbatar da wannan niyya na mahaifinsa ya gyara makarantar da masallacin domin cika masa niyyar tasa.

Ya ce gode wa Allah da ƙaddamar da buɗe makarantar da masallacin da cika wa mahaifinsu niyya na tabbatar da wannan makaranta a matsayin kyauta da kuma saka ta a matsayin Waƙafi ga mahaifin nasu.

Hon. Aminu Aminu Maifamfo ya ce sun kafa kwamiti da za su kula da makarantar tare da damƙa ta a hannun gwamnatin jihar Kano domin mutane su sami sauƙin yin karatu kyauta a makarantar.

Sannan suna da shirin samar da Islamiyya da ƙirƙiro hanyoyi da za a taimaka wa ɗalibai koyon yin sana’o’i na hannu, kuma za su cigaba da bayar da duk wata gudunmuwa a gwamnatance da kuma nasu nakan su domin cigaban makarantar.

Hon. Aminu Aminu Maifamfo ya ce yana cikin matuƙar farin ciki na cika wa mahaifinsa wannan niyya da alƙawari, domin duk wani da yake so ya tabbatar cewa ya zama ɗa nagari yayi  abin alheri ga iyayensa shi ya gode wa Allah da wannan dama da ya ba shi na cika wannan niyya.

Hon. Aminu Aminu ya yi kira da cewa ya kamata mutane su riƙa ɗaukar irin wannan ayyuka ya zama abin koyi, kuma duk lokacin da kake tasowa kake manyanta ka riƙa yin abin da na baya za su riƙa amfana na alkhairi. “Don haka matasa su ɗauki hanyoyi da zai sa a sa masu albarka da kyautatawa rayuwar al’umma.” 

By ukarofi